An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara
Lamarin ya faru ne a lokacin suke ƙoƙarin gyaran tayar ne wasu ’yan bindiga biyar suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta.
Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.
An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu matsalar tayar motar a kusa da unguwar.
- ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno
- Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore
A yayin da suke ƙoƙarin gyaran tayar ne wasu ’yan bindiga biyar suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta.
Waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu a harin, an bayyana sunayen su da: Alhaji Abdulrazak Ewenla ɗan ƙauyen Ajia da Jimoh Audu daga Gammu.
Mutanen ukun da aka sace sun haɗa da: Kazeem Ajide da Wahidi da Mufutau, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da sunayen mutanen biyu ba.
Bayan afkuwar lamarin, an tura tawagar jami’an ’yan sanda da sojoji da ’yan banga zuwa wurin da lamarin ya afku don tabbatar da tsaro tare da dawo da zaman lafiya.
Rundunar ’yan sandan jihar a cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Adetoun Ejire-Adeymi ya fitar a ranar Alhamis, ta tabbatar da faruwar harin.
Sai dai ta yi watsi da wani faifan bidiyo da ke nuna cewa mazauna ƙauyen sun tsere, lamarin da ya haifar da tunanin an ƙauracewa garin.