An kashe matashi an binne shi a dakinsa
An yi wa wani matashi dan shekara 25 mai suna Rabi’u Adamu wanda aka fi sani da Bamanga a unguwar share-wuri-zauna mai suna Ruga, kusa da babban filin kwallo na kasa da ke Abuja kisan gilla. Mahaifin marigayi Bamanga mai suna Malam Adamu Isyaku ya shaida wa ‘yan sanda, da sauran jama’a cewa, “Marigayin dana […]
An yi wa wani matashi dan shekara 25 mai suna Rabi’u Adamu wanda aka fi sani da Bamanga a unguwar share-wuri-zauna mai suna Ruga, kusa da babban filin kwallo na kasa da ke Abuja kisan gilla.
Mahaifin marigayi Bamanga mai suna Malam Adamu Isyaku ya shaida wa ‘yan sanda, da sauran jama’a cewa, “Marigayin dana ne, kuma mu mutanen garin Numan ne da ke Jihar Adamawa. Kuma na amince da a yi jana’izar marigayin, domin mun shaida cewa lallai shi ne aka yi wa kisan gilla,” a cewarsa.
Likitan da ya jagoranci hako gawar da aka binne a cikin dakin ya shaidawa mahaifin da kawun marigayin, Alhaji Abdullahi Bello Yola da sauran yayye da kannen marigayin cewa an yi masa yankan rago ne a wuyansa, an kuma caccaka masa wuka har sau hudu a kirjinsa wanda ya yi sanadiyar rasa ran nasa. An tono shi ne ranar Asabar da rana, har ya kumbura ya fara tsutsa, sannan aka birne shi. Ana zargin ya kai kwanaki hudu kafin aka tono shi.
Bugu da kari makwabtan marigayin sun ce, kila an kashe shi ne da daren Litinin ko kuma da safiyar Talata domin an kunna injin dinsa na lantarki (janareto) tun daren Litini har zuwa tsakar ranar Talata haka kuma an kunna tare da kure karan rediyonsa. An shaidawa Aminiya cewa, bayan kwanaki biyu ba a ganshi ba, sai wasu suka ce sun ga makullin kofar dakinsa a bude, sai wasu suka shaidawa shugaban yankin inda shi kuma ya shaidawa ‘yan sanda.
Babban jami’in ‘yan sanda mai kula da Wuye ya tabbatar da faruwar al’amarin sannan, ya ce kuma tuni sun damke wasu da ake zargi da kisan su biyar, da suka hada da Muktari Kano da Zahrain Awwal da Muhammad Salisu Gunners da Hassan Janare da kuma Halilu Musa Bagobiri.
Hakimin Karmajiji, Alhaji Yunusa Bako Abdullahi ne ya jagoranci jama’a don yin sallar jana’iza, sannan ya hori talakawansa da su zama masu bin doka da oda da kuma daina yi wa doka karan tsaye. Shi dai marigayi Bamanga ya na aiki ne da wata kungiyar sa kai mai suna, Heartland Alliance International. Ruga dai unguwa ce da akasarin mazaunanta leburori ne da mata masu zaman-kansu, inda babu dakin ginin bulon siminti ko na kasa, sai dai dakunan wucin-gadi da aka gina da katako aka sanya kwali sannan aka lullube da leda maganin ruwan sama da sauransu.