An kashe matashi kan batanci ga Annabi (SAW) a Bauchi

Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kashe wani mutum da ake zargin sa da yin batanci Annabi Muhammadu (SAW) a Bauchi

An kashe matashi kan batanci ga Annabi (SAW) a Bauchi

An yi wa wani matashi dukan kawo wuka har ya mutu saboda zargin sa da yin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) a Jihar Bauchi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa matashin ya mutu ne bayan da wasu matasa suka yi masa dukan da ya yi ajalinsa ranar Larabar da ta gabata a yankin Nasaru da ke Karamar Hukumar Ningi ta jihar bisa zargin sa da aikata sabo da yin kalaman batanci ga Fiyayyen Halitta (SAW).

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya sanar cewa rundunar ta yi matukar bakin ciki faruwar lamarin a kauyen Nasaru a ranar 19 ga watan Yuni, 2024.

“An shaida mana cewa wani mutum mai suna Usmanu suna muhawara game da wani sabon abu na addini da aka sani da kungiyar ’yan Faira suke yi.

“Abin takaici, wannan ya haifar da tashin hankali da hatsaniya, wanda ya yi sanadiyyar rasa ransa,” in ji shi.

Wakil ya ce, kwamishinan ’yan sanda, Auwal Musa Muhammad, ya yi Allah wadai da abin da ya faru tare da jaddada muhimmancin bin doka da oda.

Ya bayyana kudirin rundunar na kara kaimi wajen sa ido domin tabbatar da tsaro ga dukkan mazauna yankin.

Ya shawarci jama’a da su yi aiki kafada da kafada da hukumomi domin tabbatar da doka da oda, kuma su guji daukar doka a hannunsu.

Ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da fargaba ba, domin an samu zaman lafiya a yankin da lamarin ya shafa.

Rahotanni sun ce an kashe wanda ake zargin ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Laraba bayan wata takaddama kan wata kungiyar addini.

Lamarin dai ya ja hankalin mutane da dama da ke kusa da wurin inda suka rika bin muhawara a tsakaninsu.

Wani ganau ya ce, “wanda aka kashe dan kungiyar Faira ne, kuma an ji shi yana fadin kalaman batanci ga Annabi (SAW).

“Hakan ya sa samari suka kalubalance shi da cewa ya janye maganarsa, amma ya dage cewa ba zai yi ba, har ma ya maimaita.

“Daga nan ne suka fara lakada masa duka.”

Wani wanda aka yi abin a idonsa ya ce mutanen yankin da ’yan sanda sun yi kokarin ceto Yunusa, amma sai matasan dauke da duwatsu, sanduna da sauran abubuwa masu hadari, suka ci karfinsu, har suka kai masa hari har ya mutu.