An kashe matashi kan rigimar lika hoton Nyass a masallaci
A ranar Asabar da ta gabata wani matashi mai suna Auwal Musa ya rasa ransa sakamakon rigimar da ta barke a kan limanci a masallacin Gida Bulo da ake gab da kammala gininsa a unguwar Rimin Kebe a karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano. Rahotanni sun ce rigimar ta samo asali ne a lokacin da […]
A ranar Asabar da ta gabata wani matashi mai suna Auwal Musa ya rasa ransa sakamakon rigimar da ta barke a kan limanci a masallacin Gida Bulo da ake gab da kammala gininsa a unguwar Rimin Kebe a karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano.
Rahotanni sun ce rigimar ta samo asali ne a lokacin da wasu matasa suka yayyage hotunan Sheikh Ibrahim Inyass da wani malami mai suna Alhassan bin Abubakar (Fatahu Rabbani) ya lika a masallachin a lokacin da ya gudanar da maulidi.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa yage hotunan Sheikh Inyass ne ya harzuka magoya bayan Malam Fatahu Rabbani inda suka koma da niyyar sake lika wasu, a nan ne wasu matasan unguwar suka ki amincewa, lamarin da
ya kai su ga ba hammata iska har matashin mai suna Auwal ya rasa ransa.
“Ganin Malam Alhassan ya yi maulidi a masallachin har da lillika hotunan Sheikh Inyass sai matasan unguwar suka yi zaton cewa ya yi haka ne don ya karbe limancin masallacin daga ainihin limamin masallacin mai suna Malam dahiru. Hakan ya sa suka yage hotunan, su kuma magoya bayan Malam Alhasan suka harzuka har aka yi rigimar da ta jawo asarar rai,” inji majiyarmu.
Aminiya ta gano cewa Malam dahiru ya kwashe shekara 27 yana limanci a masallacin tun lokacin yana fili.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mahaifin matashin ne ya sanar da rundunarsu game da kashe dansa. “Mun je mun duba gawarsa mun ga shaidar raunuka a jikinsa, kuma mun mika gawar zuwa asibiti don gano musababbin mutuwarsa, kuma muna ci gaba da bincike a kan lamarin,” inji shi.