An kashe matashi saboda hula a Bauchi

Har gida suka je suka dauke shi daga bisani dai gawarsa aka nuna wa mahaifansa

An kashe matashi saboda hula a Bauchi

Gawa

An kashe wani matashi mai shekaru 19 mai suna Suleiman Shu’aibu Fagarau da ke sana’ar wankin huluna saboda bacewar wasu huluna guda biyu.

Mahaifin mamacin, Dokta Shuaibu Sarkin Fagarau, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su bi musu hakkinsu, kuma suyi musu adalci

Dokta Shu’aibu ya shiada wa ’yani jarida da cewa “Marigayi Sulaimanu yana aiki a shagon Malam Awisu Maiwakin Hula.

“Yana aikin wankin hula ranan Laraba ya ba shi wankin huluna guda 10 ya je ya wanke masa a gida da safe ya kai a sa akwari.

“Da ya wanke ya je sawa a kwari sai suka ga huluna sun zamo guda 8 ba guda 10 ba, sai ya tambaye shi ina sauran kwaya biyun?

“Sai ya ce masa shi ma su kadai ya gani. Ya tambaye shi ya ce shi dai abin da ya gani ke nan, amna bari ya koma gida ya gani ko zai gani.

“Da ya koma gida ya fada wa mahaifiyansa ga yadda suka yi da mai gidansa amma bari ya duba.

“Da ya duba bai gani ba, sai na dauko wata roba nace sai na zane shi na fara dukan sa, sai yayana ya ce ‘ka yi hakuri kar ka doke shi ba maganan duka ba ne abincike shi kawai aji yadda huluna suka yi’.”

Mahaifin yaron ya ce, “Muna cikin magana sai shi maigindan nasa Malam Awaisun ya zo, nace na bincika huluna babu, zan ma yi masa hukunci aka hana ni aka ce abincika tukuna.

“Sai maigidan nasa yake cewa tunda suke tare da shi bai taba sanin wani abu na rashin gaskiya a tsakaninsu ba.

“Ya ce duk yaran shagonsa ba mai gaskiya da amanansa, ya ce mabudin shagonsu ma a hannunsa yake shi yake budewa da safe, shi ne kuma yake rufewa idan sun tashi, amma mu bar shi zai bincika.

“Na ce to ya je ya bincika, in ma ta kama ku je zuwa wajen hukuma, amma in kuka je zuwa ga hukuma in abin ya gagara ka dawo gida za mu warware a gida tunda haka abin yake batun huluna biyu ba zai zama abin tashin hankali ba.”

Malam Shuaibu ya ce, “Ina zaune agida har lokacin fitana ya yi bai zo ba, sai na je na same shi a shago, na ce masa ban ji ku ba, ni kuma ina so in fita kasuwa?

“Ya ce to ba damuwa in ba shi lambar wayata, idan da bukata zai kira ni.

“Na tafi kasuwa ban sake tuna maganar ba, sai da magariba dan uwana ya ce har yanzu bai ga yaron ya dawo ba.”

Ya c, “Bayan na fita sai maigidansan, Malam Uwaisu suka zo da wani suka dauke shi, a mashin sai shi ya kira shi ya ce masa yana dawowa.

“Da ba su dawo ba sai ya kira shi maigidan nasa, ya ce amma abin da ya faru sun kirashi ne, da suka kai shi, sai suka bubbuge shi sun sa masa tiyagas wani kumfa na fita a bakinsa, sun dauke shi sun kai shi asibiti.”

Mahaifin yaron ya ce amma, “Ni kuma da na kira shi sai ya ce mini sun kai shi ne ofishin ’yan banga na Inkil, yana can Inkil din.

“Ni kuma naje ofishinsu na inkil, na kai awa uku na tambayw shi Jami’in Mulki na Ofishin, ya ce sub a a kawo wannan batu wurinsu ba.

“Sai jami’in ya kira shi bai zo ba, a karshe ma sai ya kashe wayansa, daga baya na sake kiran sa yace min yaro yana Asibitin Kwararru na Jihar Bauchi.

“Na dauki yayana muka tafi asibitin, muka je muka sami likitan, ya ce, tun daga Azahar har zuwa karfe 10 na dare a dakin bada agajin gaggawa na asibitin ya ce ba a kawo wani abu makamancin haka ba,”

Mahaifin mamacin ya ce, “Bayan mun dawo sai dan sanda ya kira ni da lambar shi Malam Uwaisu, ya ce ka zo ofishin ’yan sanda na cikin gari, da muka je ya ce min kai ne mahaifin wannan yaro nace, eh.

“Ya ce ga shi nan an kawo mana gawansa, ya ce Malam Awisu da wani wanda ake ce masa Checheniya su suka kawo gawan, kuma mun rike su,” in ji shi.

Dan sandan ya ce amma su ma basu san wani abu ba game da al’amarin.

Kafin nan itama mahaifiyar yaron tace ta kira shi Malam Awisu, kuma sun tabbatar mata cewa sun bibbige shi yana nan bakinsa na fitar da kumfa.

Malam Shuaibu ya ce, “Da ’yan sanda suka fada mini, bayan munyi salati mun sanar da Ubangiji, sai muka roki a kaishi asibiti a yi masa binciken kwakwaf ko za a gano me ya kashe shi.

“Aka mana izini aka je aka bincika, sai aka ba mu bayanin hoton da aka dauka an bibbigeshi kafofinsa biyu duk an kakkarya, yatsunsa na hannayensa biyu duk sun kakkarya, kasusuwan hakarkarinsa sun kakkarya, hatta hantarsa ta tabu wanda hakan yana nuna mana ya sha wahala an yi masa kisan walakanci.”

Ya ce daga nan ’yan sanda suka ba mu gawar suka ce za su bincika, suka ce idan an gama ta’aziyya mu dawo mu ga baturen ’yan sanda kan al’amarin.

Mahaifin yaron ya ce ba wanda yake zargi da kashe dan nasa sai mutanen da suka dauke shi a gida lafiya, kuma suka kai gawansa wa ’yan sanda.

Ya ce yana rokon gwamnati da dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro da su taimaka a yi wa dan nasa da aka kashe adalci, kuma abi masa hakkinsa.

Duk kokarin da wakilin Aminiya yayi don jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Bauchi, Supritanda Mohammed Ahmed Wakil, bai yi nasara ba.

Saboda baya ofis kuma duk kiran da aka masa ta waya baya kusa da wayan, kuma bai amsa rubutattun sakonnin da aka aika masa ba har zuwa lokacin da muke hada wannan rahoto.

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025