An kashe Musulmi a Indiya don ya hana sa waka a sabuwar shekara
An yi wa wani Musulmi dukan kawo wuka har ya rasu a Jharkhand da ke gabashin Indiya, bayan da ya bukaci wadansu mutane su rage amon wakar da suka kunna a ranar sabuwar shekara. Al’amarin ya faru ne a Mandar, wani gari a kusa da birnin Ranchi, inda a ranar Talatar da ta gabata mutane […]

An yi wa wani Musulmi dukan kawo wuka har ya rasu a Jharkhand da ke gabashin Indiya, bayan da ya bukaci wadansu mutane su rage amon wakar da suka kunna a ranar sabuwar shekara.
Al’amarin ya faru ne a Mandar, wani gari a kusa da birnin Ranchi, inda a ranar Talatar da ta gabata mutane suka rufe wata hanyar mota suna bukatar a kama wadanda suke da hannu cikin lamarin, sai dai ’yan sanda sun tarwatsa mutanen.
An kara tura ’yan sanda yankin domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da mabiya addinin Hindu.
Waseem Ansari mai shekara 19, da ke aikin leburanci a Pune ya koma kauyensu ne kwana biyu kafin kisansa. Wani babban jami’in ’yan sanda ya tabbatar wa sashin Hindu na BBC, faruwar lamarin inda ya ce: “Binciken da muka yi ya tabbatar da cewa mutanen sun kure karar wakar da suka sa ne a ranar sabuwar shekara. Kuma Waseem Ansari da abokansa biyu sun bukaci mutanen su rage karar wakar, inda hakan ya janyo sa-in-sa har mutanen suka rufar wa Waseem. Ana ganin an daba masa wani abu mai kaifi da ake amfani da shi wajen girki. Mun bukaci al’ummomin biyu su zauna lafiya. Kuma za a kama wadanda ake zargi da hannu cikin lamarin nan ba da dadewa ba.”
Hasibul Ansari wani mazaunin kauyen da abin ya faru ya shaida wa BBC cewa, “Mutanen suna zaune ne a kusa da inda Musulmi suke. Lokacin da Waseem ya shaida musu su kashe sai suka kashe shi.”
Ya kara da cewa, “Wani abokinsa ya auna arziki bayan da ya tsallake rijiya da baya. Na tabbata da bai tsere ba shi ma sai sun kashe shi.”