An kashe mutane 6 a rikicin iyakar Benuwe da Ebonyi

Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu da raunata wasu a wani rikicin iyaka a tsakanin ‘yan kabilar Igala na jihar Benuwe da kuma jama’ar Mgbo dake karamar Hukumar Ohankwu a jihar  Ebonyi. Majiyarmu ta gano cewa, an lalata amfanin gonakin jama’ar yankin yayin da jama’a da dama suka yi hijira daga gidajensu saboda rikicin. […]

An kashe mutane 6 a rikicin iyakar Benuwe da Ebonyi

Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu da raunata wasu a wani rikicin iyaka a tsakanin ‘yan kabilar Igala na jihar Benuwe da kuma jama’ar Mgbo dake karamar Hukumar Ohankwu a jihar  Ebonyi.

Majiyarmu ta gano cewa, an lalata amfanin gonakin jama’ar yankin yayin da jama’a da dama suka yi hijira daga gidajensu saboda rikicin.

Wani mazaunin unguwar da rikicin ya shafa ya ce, da farkon fara rikicin wasu matasa ne da safiyar ranar Litinin suka farwa unguwannin Agali.