An kashe mutum 1 da yin garkuwa da fasinjoji 12 a hanyar Abuja

‘Yan bindiga sun kashe wata mata daya tare da yin garkuwa da fasinjoji 12 da suke cikin wata motar bas mai kujeru 18 a kauyen Omoko da ke hanyar Abuja zuwa Lokoja. Kauyen Omoko ya nada nisan kilomita 4 zuwa garin Abaji karamar hukuma a Abuja kuma ya nada iyaka da jihar Kogi. Wani da […]

An kashe mutum 1 da yin garkuwa da fasinjoji 12 a hanyar Abuja

‘Yan bindiga sun kashe wata mata daya tare da yin garkuwa da fasinjoji 12 da suke cikin wata motar bas mai kujeru 18 a kauyen Omoko da ke hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Kauyen Omoko ya nada nisan kilomita 4 zuwa garin Abaji karamar hukuma a Abuja kuma ya nada iyaka da jihar Kogi.

Wani da ya tsallake rijiya da baya bayan an harbe shi a ciki mai suna Adesoji Rufus, ya ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 4 na yamma lokacin da suke hanyar su daga Legas zuwa Abuja.