An kashe mutum 10 a sabon harin Kudancin Kaduna
Akalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wadansu da dama suka jikkata ciki har da mata da yara a wani hari da wadansu dauke da bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai a Ungwan Pah II da ke kauyen Gwandara a Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna […]
IGP
Akalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wadansu da dama suka jikkata ciki har da mata da yara a wani hari da wadansu dauke da bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai a Ungwan Pah II da ke kauyen Gwandara a Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna ranar Lahadi da daddare.
Sai dai wadansu ganau sun ce adadin wadanda suka rasa rayukan nasu ya haura 15. Yayin da Aminiya ta garzaya babban asibitin Kafanchan ta samu zantawa da wadanda suka tsira da raunukan harsasai da ke cinya a asibitin.
Daya daga cikin wanda ya tsira da harbin bindiga a hannunsa mai suna Peter Joshua daga garin Gwandara ya shaida wa Aminiya cewa suna zaune da misalin karfe takwas zuwa tara na dare sai kawai suka ji karar harbin bindiga a unguwar da ke makwabtaka da su mai suna Pah II inda suka runtuma don neman tsira.
“Garin guduwa ne suka harbe ni inda harsashi ya same ni a hannu da kafa,” inji shi.
Peter ya ce ba su taba yin rikici tsakanin manoma da makiyaya ba a garin sai dai makwabtansu da suka taba samun matsala da makiyaya. Ya ce a cikin daren ’yan sanda suka kwaso su zuwa asibitin Kafanchan.
Wata da aka yi abin a kan idonta mai suna Bictoria Musa ta ce suna zaune suna gudanar da biki a kauyen sai kawai wadansu mahara su uku suka bayyana da bindigoginsu inda babu wata-wata suka bude musu wuta.
“Nan take wuri ya hargitse kowa ya fara gudun tsera da ransa. An karkashe masu karancin kwana da dama. Yanzu ga mu a asibiti da gawa biyar kuma mun baro wasu gawarwaki tara kwance a can,” inji ta.
Yayin da suke amsa tambayar Aminiya a lokuta daban-daban a harabar asibitn na Kafanchan, Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Jama’a wanda ya wakilci shugaban wanda ba ya gari, Micah Tanko Ngboni da wakilin Sanatan Kudancin Kaduna kuma Babban Mai taimaka masa, Joseph Major Baba sun bayyana alhininsu da faruwar lamarin, inda suka yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu domin gwamnati ba za ta kyale lamarin ya tafi haka kawai ba.
Yayin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce zuwa lokacin suna da adadin mutum 10 ne da suka rasu yayin da wadansu da dama suka jikkata. Ya ce zuwa yanzu Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ahmad Abdurrahman ya bayar da umarni inda jami’ansu suka bi bayan maharan cikin dazukan yankin tare da shan alwashin zakulo su.
“A yanzu komai ya lafa kuma muna sanar da jama’a su kwantar da hankalinsu domin tuni gamin- gambizar jami’an tsaro suka bazama neman maharan, kuma muna tabbatar wa jama’a cewa duk wanda ya shiga hannunmu zai dandana kudarsa tare da fuskantar shari’a,” ijin shi.
Idan za a iya tunawa a watan da jiya an kai wa wadansu Fulani makiyaya hari a kauyen Gindin Dutse da ke gab da inda wannan lamarin ya faru, inda aka kashe mutum biyar daga cikin Fulanin tare da jefa gawarwakinsu a cikin wata rijiya.