An kashe mutum 10 a sabon rikici a Riyom

Wani sabon rikici da ya barke a karamar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato ya jawo asarar rayukan akalla mutum goma da kuma aka kone gidaje da wata majami’a tare da kashe shanu masu yawa.Gidan rediyon BBC Landan ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa lamarin ya faru ne a kauyukan Jol da Tanjo da ke […]

An kashe mutum 10 a sabon rikici a Riyom
An kashe mutum 10 a sabon rikici a Riyom

Wani sabon rikici da ya barke a karamar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato ya jawo asarar rayukan akalla mutum goma da kuma aka kone gidaje da wata majami’a tare da kashe shanu masu yawa.
Gidan rediyon BBC Landan ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa lamarin ya faru ne a kauyukan Jol da Tanjo da ke yankin Riyom, inda Fulani da ’yan kabilar Berom ke zargin juna da haddasa rikicin.
Tun a ranar Litinin da ta gabata ne aka shiga zaman dardar a Riyom, bayan wani hari da aka kai kan Fulani makiyaya kuma aka kashe shanu da dama, lamarin da ya kara ta’azzara daga daren Talata zuwa wayewar garin Larabar.
Shugaban matasan kabilar Berom, Mista Rwang Dalyop Dantong, ya shaida wa BBC cewa wasu mahara da ake zargin Fulani ne suka kai hari a daren jiya (Talata) zuwa wayewar yau (Laraba), a kauyen Tanjol inda suka kona gine-gine da dama, kuma suka kashe ’yan kabilar Berom biyar da sojoji biyar bayan sun yi musayar wuta.
Sai dai Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Filato, Alhaji Haruna Boro Husseini, ya musanta hannun Fulani a harin na Riyom, amma ya ce abin da ya sani shi ne ’yan kabilar Berom sun kashe shanun Fulani da dama kuma sun sace wasu bayan jikkata wasu makiyaya a ranar Litinin.