An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Binuwai
Jama’a da sauran masu ruwa da tsaki a jihar sun yi kira ga hukumomin tsaro da ɗauki matakan da duka dace.
Aƙalla mutum 10 ne aka ruwaito sun rasu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Saai da ke gundumar Mbajir, a Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala ta Jihar Binuwai.
Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga ƙauyen ne cikin dare, inda suka riƙa harbe-harbe.
- Mutanen gari sun fatattaki ’yan bindiga tare da kashe 4 daga cikinsu a Katsina
- Jigawa na samar da kashi 40 na alkamar da ake nomawa a Najeriya – Shettima
Sun ce an gano gawarwaki aƙalla mutum 10, sai dai alƙaluman da hukumomi suka bayar ya bambanta da wannan.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutane sun farka ne sakamakon ƙarar harbe-harbe, inda suka riƙa gudu domin tsira da rayukansu.
Ya ce wasu daga cikin mutanen an harbe su, yayin da aka kashe wasu da adda.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na jihar Binuwai, Alhaji Ardo Risku Muhammad.
An yi masa kwanton-ɓauna ne yayin da yake dawowa daga taron sulhu da ’yan sanda suka shirya tsakanin makiyaya da manoma a Ƙaramar Hukumar Ohimini.
Haka kuma an kashe abokin tafiyarsa, Yakubu Isah, a harin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala, Justine Shaku, ya tabbatar da aukuwar harin, amma ya ce mutane shida ne suka mutu.
Ita ma kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu.
Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya yi Allah-wadai da harin.
Ya umarci jami’an tsaro su tura ƙarin dakaru zuwa ƙauyen Saai da sauran yankuna, sannan su kamo waɗanda suka kai harin.
An sace fasto da wasu mutum 2
A wani labarin kuma, wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da Rabaran Dokta Samuel Gbinde tare da wasu mambobin coci biyu daga gidan limaman Cocin NKST da ke Andyar-Ishan, a Ƙaramar Hukumar Guma ta jihar Binuwai.
Cocin ta tabbatar da sace mutanen a cikin wata sanarwa, inda ta buƙaci mambobinta da sauran jama’a su yi addu’a domin a kuɓutar da su cikin ƙoshin lafiya.
Haka kuma ta roƙi jami’an tsaro da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar su ƙara ƙoƙari wajen ceto waɗanda aka sace tare da kamo masu laifin.
’Yan siyasa sun buƙaci a ɗauki mataki
Ɗan takarar gwamnan Jihar Binuwai na jam’iyyar PDP a zaɓen 2027, Michael Aondoakaa (SAN), da shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro, sun yi Allah-wadai da kashe-kashe a jihar.
Sun buƙaci jami’an tsaro su gudanar da bincike, su kamo waɗanda ke da hannu a hare-haren, tare da ɗaukar matakan gaggawa domin kawo ƙarshen tashe-tashen hankula a Jihar Binuwai.