An kashe mutum 100 a sabon rikicin kabilanci a Jihar Nasarawa
Sama da mutum 100 ne aka hallaka a kauyen Igah da ke karamar Hukumar Nasarawan Eggon da ke Jihar Nasarawa sakamakon fadan da ya sake barkewa tsakanin al’ummar Eggon da Gwandara a karshen makon da ya gabata. Wani mazaunin kauyen da lamarin ya auku a kan idonsa wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida […]

Sama da mutum 100 ne aka hallaka a kauyen Igah da ke karamar Hukumar Nasarawan Eggon da ke Jihar Nasarawa sakamakon fadan da ya sake barkewa tsakanin al’ummar Eggon da Gwandara a karshen makon da ya gabata.
Wani mazaunin kauyen da lamarin ya auku a kan idonsa wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa fadan ya auku ne sakamakon gardamar da kabilun biyu ke yi a kan mallakar wani filin noma da ke yankin. Ya ce “ Da rikicin ya yi tsanani sai aka kai maganar ga masu unguwanni da dagatan yankin. Amma duk da haka ba a iya magance rikicin ba. Daga nan aka soma ba hamata iska tsakanin matasan kabilun biyu kafin a kai ga amfani da makamai ana ta kashe-kashe.”
Wakilinmu dai ya lura cewa mata da yara ne aka fi kashewa a yayin rikicin kasancewar gawarwakinsu ne suka fi yawa a Asibitin kwararru na dalhatu Araf da ke Lafiya.
A halin yanzu jama’a da dama daga yankin musamman mata da yara, sun yi gudun hijira zuwa wasu garurruwa da ke makwabtaka da suka hada da Nasarawa Eggon da Burum-burum da Basa da Shabu da Akwanga da sauransu.
Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura da shuga-bannin hukumomin tsaron jihar sun gudanar da wani taron tsaro na gaggawa game da lamarin a gidan gwamnati, inda suka sha alwashin kawo karshen rikicin da sauran rigirgimun da suka ki ci, suka ki cinyewa a jihar ta hanyar bullo da wasu dabaru da suka hada da tura isassun jami’an tsaro zuwa yankin da sauran yankunan da ake samun rigirgimu a jihar da kuma sanar da Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da aukuwar lamarin don ya taimaka wa jihar wajen kawo karshen tashin-tashinar.