An kashe mutum 11 a Afganistan
An kashe mutane 11 a wani hari da aka kai jiya Alhamis akan wani gidan saukar baki a Kabul, babban birnin kasar Afganistan. Wani Ba’amurke na cikin wadanda aka kashe, kuma da dama daga cikinsu na halartar wata liyafa ne a otal din mai suna, Park Palace. Jakadan Indiya a Kabul ya ce akwai ‘yan […]
An kashe mutane 11 a wani hari da aka kai jiya Alhamis akan wani gidan saukar baki a Kabul, babban birnin kasar Afganistan.
Wani Ba’amurke na cikin wadanda aka kashe, kuma da dama daga cikinsu na halartar wata liyafa ne a otal din mai suna, Park Palace. Jakadan Indiya a Kabul ya ce akwai ‘yan kasarsa da dama cikin wadanda harin ya shafa
‘Yan sanda sun dauki sa’oi biyar kafin su karbe gidan, sannan sun sami nasarar kubutar da mutane fiye da 50.
Cikin wadanda suka rasa rayukansu har da ‘yan bindigar biyu, bayan sun kasa tashin bam din da suke dauke da shi. Kodayake, babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma a ‘yan makonnin nan, kungiyar Taliban ta zafafa hare-harenta a Kabul dama wasu wurare a kasar.
Har ila yau, ko a farkon watan nan sai da aka kashe ‘yan sanda 17 a wani hari da ‘yan kungiyar Taliban suka kai a arewacin yankin Badakhshan.