An kashe mutum 11 a sabon rikici a Kudancin Chadi
Manoman na zargin makiyaya da barin dabbobinsu da yi musu barna da gangan.
‘Yan bindiga sun kashe mazauna kauyuka 11 a kudancin Chadi, a yankin da ke fama da rikici tsakanin makiyaya da manoma, in ji sojoji a ranar Alhamis.
Harin dai ya faru ne a ranar Laraba, a daidai lokacin da kasar Chadi ta sanar da cewa ta hade da makwabciyarta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) a wani farmakin da ba a taba ganin irinsa ba.
- DSS ta tabbatar da tsare Baffa Hotoro kan batanci ga Annabi
- Muna binciken gwamnan Zamfara kan N70bn —EFCC
Ministan tsaron kasar, Daoud Yaya Ibrahim ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, ’yan bindiga sun kai hari kauyen Mankade da ke gundumar Laramanaye, inda suka kashe mutane 11 tare da yin awon gaba da shanunsu.
“Jami’an tsaro sun bi sahunsu, inda suka kashe ’yan bindiga bakwai tare da kama wasu takwas,” in ji shi.
Mataimakin Laramanaye, Djimet Blama Souck, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa (AFP) cewa an kashe mutanen kauyuka 12 da suka hada da mata da yara.
A ranar 8 ga watan Mayu, mazauna kauyuka 17 a yankin sun mutu a wani hari makamancin haka, wanda sojojin Chadi suka dora alhakinsa kan “‘yan bindiga” na Chadi da suka tsallako daga CAR.
A ranar Laraba, ministan tsaron kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa (AFP) cewa, a makon da ya gabata sojoji sun bi maharan a kan iyakar kasar, tare da hadin gwiwa da sojojin kasar CAR sun kashe kusan goma daga cikinsu.
Yanzu haka dai an kawo karshen wannan farmakin, in ji shi a ranar Alhamis, inda ya kara da cewa “an kashe barayi da dama,” kuma sojojin Chadi sun koma gida da fursunoni 30 da shanu 130 da aka sace.
A Bangui kuwa, babban birnin kasar CAR, wani mai taimaka wa shugaba Faustin Archange Touadera, ya tabbatar da cewa kasashen biyu sun yanke shawarar yin hadaka don murkushe ‘yan bindigar.
“Makonni biyu da suka gabata, tawagogin biyu daga hedikwatar sojojin Chadi da na CAR sun gana don tsara matakin soji na hadin gwiwa,” in ji Fidele Gouandjika, minista kuma mai ba da shawara na musamman ga Touadera.
Touadera da shugaban Chadi Janar Mahamat Idriss Deby “sun dauki matakin hadin gwiwa don kawar da ‘yan bindiga a bangarorin biyu na kan iyaka,” in ji shi.
Dangantaka tsakanin CAR da Chadi, biyu daga cikin kasashe mafi talauci da tashin hankali a duniya, ta sha yin tsami.
Hakan na da nasaba da zargin junan da ake yi cewa wata kasa tana da ‘yan tawaye masu dauke da makamai.
Yankunan kan iyaka na Chadi, Kamaru da CAR sun fuskanci arangama tsakanin makiyaya da galibinsu Musulmi ne da kuma manoma masu zaman kashe wando wadanda galibi Kiristoci.
Sau da yawa manoman na zargin makiyayan da barin shanunsu suna tattake amfanin gonakinsu suna cinye su, yayin da makiyayan suka ce suna da hakkin yin kiwo a gonakin nasu.