An kashe mutum 15 a sabon hari a Binuwai
Shaidu sun ce an gano gawarwaki 14 bayan harin a yankin Efeyi-Ugboju baya ga wani mutum guda da aka kash a yankin Ipom a ranar Litinin.
Mutum 15 sun mutu a wani sabon hari da aka kai a yankin Ugboju da ke Karamar Hukumar Otukpo ta Jihar Binuwai a ranar Talata.
Shaidu sun ce an gano gawarwaki 14 bayan harin a yankin Efeyi-Ugboju baya ga wani mutum guda da aka kash a yankin Ipom a ranar Litinin.
Sun ce adadin mutanen da aka kashe a harin Efeyi na iya karuwa a yayin da ake ci gaba da neman gawarwaki zuwa karfe 11:30 na safiyar Talata, baya ga wasu da dama da ke samun kulawa a asibiti a sakamakon rauni da suka samu daga harin.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun dauki sa’o’i sun cin karen su babu babbaka, “tun daga misalin karfe 5 na asubu zuwa 9 na safiyar Talata.
- Shugaban Mazaɓar Pantami ya fice daga APC
- Kotun daukaka kara ta soke hukuncin soke rajistar Jam’iyyar ADC da wasu 4
- Hisbah ta haramta yin kayan ‘na gani ina so’ a Sakkwato
“An yi wa mutum 14 kisan gilla a Efeyi-Ugboju, a yayin da makiyayan da ake zargi suka kashe wani mutum a Ipom-Ugboju a safiyar ranar Litinin,” in ji shi.
Shugaban Karamar Hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya shaida wa manema labarai a Makurdi cewa an gano gawarwaki 14 a Efeyi-Ugboju, wasu da dama kuma an jikkata su.
Ya yi Allah wadai da harin wanda ya kira na haka kawai.
“Babu wanda ya tsokane su. Haka kawai suka shigo suka kashe mutanenmu… mutane na rayuwa cikin tsoro da rashin tabbas. Mazauna kauyuka makwabta sun fara yin kaura domin tsira da rayuwarsu,” in jni Ogiri.
Ya bayyana damuwa cewa an ci gaba da kai hare-hare, duk da an girke jami’an tsaro, da suka haɗa da sojoji da ’yan sanda da ’yan sandan kwantar da tarzoma da masu gadin daji.
Sai dai kakakin ’yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ya ce ba shi da ƙarin bayani kan lamarin.