An kashe mutum 17 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Wani sabon rikici da ya barke ranar Litinin a babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Bangui ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da wasu Fulani musulmi su 17.Rikicin ya zo ne mako biyu bayan wani tashin hankali da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21.Wani soja da ke aikin samar da zaman lafiya […]
Wani sabon rikici da ya barke ranar Litinin a babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Bangui ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da wasu Fulani musulmi su 17.
Rikicin ya zo ne mako biyu bayan wani tashin hankali da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21.
Wani soja da ke aikin samar da zaman lafiya a birnin Bangui ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa ’yan kungiyar anti-Balaka ne ke da alhakin kisan. Ya kuma ce “an yi kaca-kaca da wasu daga cikin gawarwakin, wasu kuma an kona su”. Ya ce kisan ya zo ne lokacin wani harin daukan fansa da aka kai garin da kungiyar Musulmi ta Seleka ke da rinjaye. Sojan ya ce harin ya tilasta wa mutane akalla 6000 kaurace wa muhallinsu.
Wani dan kungiyar anti-Balaka da ya zanta da Kamfanin Dillancin na AFP a birnin Bangui, ya ce ba mayakan kungiyarsu ba ne suka kai harin. Kuma ya ce matasa ne bata gari suka kai harin bisa radin kansu.