An kashe mutum 17 a sabon harin da aka kai Jihar Filato
Jami’an tsaro a Jihar Filato sun tabbatar da mutuwar mutum 17 a wani hari da wasu mutane da ba a gane ko su wane ne ba suka kai a kauyen Shonong da ke karamar Hukumar Riyom a ranar Litinin da ta gabata.Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Chris Olakpe ya shaida wa manema labarai a Jos […]
Jami’an tsaro a Jihar Filato sun tabbatar da mutuwar mutum 17 a wani hari da wasu mutane da ba a gane ko su wane ne ba suka kai a kauyen Shonong da ke karamar Hukumar Riyom a ranar Litinin da ta gabata.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Chris Olakpe ya shaida wa manema labarai a Jos cewa ana zargin Fulani da kai harin na kauyen Shonong inda aka kashe mutum 17 tare da raunata mutane da dama da kona gidaje da kayan amfanin gona.
Kwamishinan ya ce rundunar ta hada hannu da takwararta ta Jihar Kaduna don ganin an kamo wadanda suka kai harin domin a gurfanar da su a gaban shari’a.
A sanarwar da Rundunar Tsaro ta Musamman da ke aikin samar da zaman lafiya a jihar (STF) ta fitar dauke da sanya hannun kakakinta Kyaftin Salihu Mustapha, ta ce an kai hari ne da misalin karfe 9:30 na safe, inda mutanen da ke yankin suka kira jami’an rundunar ta waya suka sanar da su halin da ake ciki.
Sanarwar ta ce nan take jami’an rundunar suka isa kauyen a inda suka tarar maharan sun zagaye kauyen tare da kashe mutane da dama da kona gidaje da kayan amfanin gona. “Nan take jami’an rundunar suka nemi karin jami’an tsaro inda suka kori maharan, bayan nan ne sun jami’anmu suka gano gawarwaki tara da konannun mutum bakwai,” inji sanarwar wadda ta ce zuwa yanzu hankula sun fara kwantawa a yankin.