An kashe mutum 18 a rikicin dodanni a Imo

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar umarnin kama duk wanda yake da hannu a rikicin.

An kashe mutum 18 a rikicin dodanni a Imo

Aƙalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata, a wani rikicin ƙungiyoyin dodanni da ke gaba da juna a ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Orsu, a Jihar Imo.

Rahotanni, sun nuna cewa rikicin ya ɓarke ne, yayin wani bikin al’ada da ale gudanarwa, inda ƙabilar Ibo ke shirya wasan dodanni.

Amma abin ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka yi amfani da wannan damar wajen kai hare-hare.

Ƙauyukan da rikicin ya shafa sun haɗa da Umukabia, Eziawa, Ihitte Nasa, Umuhu, Amaoku, da Amaebe.

A cikin waɗannan ƙauyuka, an hallaka mutum 18 yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka.

Farfesa Chidi Odinkalu, Tsohon Kwamishinan kare haƙƙin ɗan Adam, ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa abin da ya faru dabbanci ne kuma abin ƙyama.

Ya ce rikicin ya fara ne a wata mashaya kafin ya bazu zuwa sauran sassan gari da ƙauyuka.

Wasu mazauna ƙauyukan da ke maƙwabtaka, sun ce sun jiyo ƙarar harbe-harbe a daren da rikicin ya faru, amma tsoron kada abin ya rutsa da su, suka kasa fitowa daga gidajensu.

Wasu shaidu, sun bayyana cewa rikicin yana alaƙa da ƙungiyoyin fafutukar kafa ƙasar Biyafara (IPOB) da kuma wata ƙungiya da ke goyon bayan haɗin kan ƙabilar Ibo.

A ƙauyen Umukabia, wasu iyalai guda uku sun rasa rayukansu, yayin da a ƙauyen Eziawa kuma mutum biyar suka mutu.

Lamarin da ya tayar da hankalin jama’a da ba su ji ba su gani ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce sun fara bincike domin gano musabbabin rikicin da kuma kama waɗanda ke da hannu a ciki.

Haka kuma, waɗanda suka jikkata an kai su asibiti, domin kula da su.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Aboki Danjuma, ya bayar da umarnin kamo duk wanda ke da hannu a rikicin domin gurfanar da su gaban shari’a.