An kashe mutum 2 a rikicin kabilanci a Kogi
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce komai ya daidaita bayan tura jami’anta yankunan biyu.
Akalla mutum biyu aka kashe sannan aka kone gidaje sama da 70 a wani rikicin kabilanci da ya barke a Jihar Kogi.
Rikicin ya barke ne tsakanin kabilar Oturpo-Ojile da Ochi-Ibadan a Karamar Hukumar Ankpa da ke jihar.
- Mutum 10 sun rasu, 12 sun ji rauni a hatsarin mota Jigawa
- Kotu ta soke belin da ta bai wa Dokta Dutsen Tanshi
Bayanai sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da wasu mazauna garin Ochi-Ibadan suka kashe wani mutum dan kabilar Oturpo-Ojile yayin da yake hanyarsa ta dawowa daga Legas zuwa Oturpo-Ojile.
Lamarin ya fusata wasu matasan kabilar Oturpo-Ojile, inda suka kai wa kabilar Ochi-Ibadan harin ramuwar gayya, tare da kone gidaje da kadarorin miliyoyin Naira.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Ankpa, Akus Lawal, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Janairu, 2024, inda ya ce rikicin kabilanci da ya barke tsakanin kabilun biyu, ya yi da matukar tayar da hankali.
Ya kuma yi kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kogi, da ta gaggauta kai kayan agaji ga wadanda rikicin ya shafa.
Shi ma da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Aya, ya ce an tura tawagar ‘yan sanda zuwa yankin don tabbatar da doka da oda.
Kazalika, ya ce ’yan daba ne suka kashe wani mutum mai Samuel Peter da kuma wani mutum guda daya.
Ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bethrand Onuoha, ya ziyarci yankunan biyu bayan lamarin ya daidaita.