An kashe mutum 2 da tarwatsa sansanin masu garkuwa a Bauchi
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kashe mutum biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Alkaleri da ke Jihar. Jami’an sun yi hakan ne bayan sa’o’i 48 da kashe wani dan fashi da makami a wani samame da suka kai kauyen Miri […]
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kashe mutum biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne tare da tarwatsa maboyar masu garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Alkaleri da ke Jihar.
Jami’an sun yi hakan ne bayan sa’o’i 48 da kashe wani dan fashi da makami a wani samame da suka kai kauyen Miri cikin karamar Hukumar Bauchi.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar ‘yan sandan jihar DSP Kamal Datti Abubakar, ne ya sanar da hakan a Bauchi, ya kuma ce jami’an ‘yan sandan sun kwato makamai da dama a samamen da suka kai maboyar.