An kashe mutum 2 da yin garkuwa da jami’an Kwastam 2 a Katsina
A wani tagwayen harin da ‘yan bindiga suka kai a karamar Hukumar Jibiya a jihar Katsina, ya bayyana cewa an kashe fararen hula biyu da yin garkuwa da wasu jami’an Kwastam biyu sannan suka harbe daya daga cikin jami’an. Rahotan na bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai harin ne cikin garin Magama a cikin Jibiya […]
A wani tagwayen harin da ‘yan bindiga suka kai a karamar Hukumar Jibiya a jihar Katsina, ya bayyana cewa an kashe fararen hula biyu da yin garkuwa da wasu jami’an Kwastam biyu sannan suka harbe daya daga cikin jami’an.
Rahotan na bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai harin ne cikin garin Magama a cikin Jibiya da yammacin ranar Talata, inda suka shiga cikin gidan wani mai suna Abu Kasim suka dauke matarsa da tagwayen ‘ya’yansa Hassan and Hussaina.
Jim kadan, da zuwan jami’an tsaro da sojoji sun yi nasarar kubutar da matar Abu Kasim da dansa Hassan.