An kashe mutum 20 a sabon harin Binuwei

’Yan bindiga sun kashe kimanin mutum 20 a harin da suka kai a kananan hukumomi biyu da ke jihar Binuwe.   Aminiya ta gano cewa  mutane da yawa sun mutu a kauyuka shida a kananan hukumomin yankin da suka hada da Logo da Gumi yayin da ’yan bindigar suka kai harin a ranar Litinin din […]

An kashe mutum 20 a sabon harin Binuwei

’Yan bindiga sun kashe kimanin mutum 20 a harin da suka kai a kananan hukumomi biyu da ke jihar Binuwe.
 
Aminiya ta gano cewa  mutane da yawa sun mutu a kauyuka shida a kananan hukumomin yankin da suka hada da Logo da Gumi yayin da ’yan bindigar suka kai harin a ranar Litinin din da ta gabata da kuma jiya.
 
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Moses Joel Yamu ya tabbatar da aukuwar lamarin amma bai bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba.