An kashe mutum 3 bayan matsafa sun kai farmaki a Bayelsa
Wani mazaunin unguwar ya shaida wa Aminiya cewa, wanda aka fara harba ɗan tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan banga ne.
Wasu da ake zargin matsafa ne ’yan ƙungiyar Greenland, sun kai farmaki kan al’ummar Igbogene da ke ƙaramar hukumar Yenagoa a Jihar Bayelsa, inda suka kashe mutum uku.
Matsafan sun kai farmakin ne a daren Laraba cikin mutum uku da suka kashe har da ɗan tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan banga a yankin, wanda aka fi sani da ‘Money Sweet’.
- Boko Haram: Zulum ya bai wa iyalan sojojin da aka kashe gudummawar N300m
- China ta ware $255m domin kammala aikin jirgin ƙasan Kano-Kaduna
Mambobin ’yan ƙungiyar asiri waɗanda adadinsu ya kai 10, ɗauke da muggan makamai. Sun mamaye yankin Igbogene ne da misalin ƙarfe 8 na dare, lamarin da ya sa mazauna yankin suka yi yunƙurin neman tsira da ransu.
A baya-bayan nan ne dai gwamnatin jihar ta mayar da dukkanin tashohin motoci da ke sufuri zuwa wasu jihohi ta koma unguwar, babu tabbas ko farmakin ‘yan ƙungiyar asirin saboda kasancewar sauya tashar motar da aka yi ne.
Wani mazaunin unguwar ya shaida wa Aminiya cewa, wanda aka fara harba ɗan tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan banga ne.
Yayin da aka harbe shi a kusa da gidan su, an harbe mutum na biyu inda ba a bayyana wurin da aka harbe shi ba kamar babban yayansa ya sanar.
Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa, harin ya samo asali ne sakamakon hamayyar da ke tsakanin fitaccen ɗan ƙungiyar asiri ta Bobos da kuma ‘yan kungiyar Greenlanders, waɗanda mambobin ƙungiyar mazauna yankin ne kuma ‘yan asalin garin Igbogene ne.
Yayin da ‘yan sanda suka ce an kashe mutane uku, mazauna unguwar sun ce biyu sun mutu a harin inda mutum na uku ke karɓar magani sakamakon harbin bindiga.