An kashe mutum 3 sanadiyyar fada akan budurwa a Bauchi

Mutum 3 aka kashe tare da raunata 18 yayin da aka kone gidaje 2 a daren ranar Lahadi lokacin da rukunin matasa biyu suka kaure da fada a Bauchi. An dai fara fadan ne sanadiyyar bikin cika shekara a yankin Lukshi da ke wajen garin Bauchi. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kamal Datti Abubakar, ya […]

An kashe mutum 3 sanadiyyar fada akan budurwa a Bauchi

Mutum 3 aka kashe tare da raunata 18 yayin da aka kone gidaje 2 a daren ranar Lahadi lokacin da rukunin matasa biyu suka kaure da fada a Bauchi.

An dai fara fadan ne sanadiyyar bikin cika shekara a yankin Lukshi da ke wajen garin Bauchi.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kamal Datti Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce an yi fada tsakanin rukunin matasa biyu akan budurwa daya.