An kashe mutum 47 da raunata wasu a Abuja – ‘Yan Shi’a

‘Yan kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya ko kuma ‘yan Shi’a sun ce, arangamar da aka yi da su da jami’an soja , ‘yan sanda makon da ya gabata ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 47. Kungiyar ta ce,  ‘yan sanda sun kama ‘yan kungiyar 156 yayin da suke gudanar da tattaki, a yanzu haka mutum dubu […]

An kashe mutum 47 da raunata wasu a Abuja – ‘Yan Shi’a

‘Yan kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya ko kuma ‘yan Shi’a sun ce, arangamar da aka yi da su da jami’an soja , ‘yan sanda makon da ya gabata ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 47.

Kungiyar ta ce,  ‘yan sanda sun kama ‘yan kungiyar 156 yayin da suke gudanar da tattaki, a yanzu haka mutum dubu xaya ne suka bace ba’a san inda suke ba.

Sheikh Abdullahi Zango, ya bayyana wa manema labarai cewa, a yanzu haka ‘yan kungiyar 106 ne suke jinya a asibitoci inda suka kashe kudi naira miliyan 8  a jinyar kuma ana bukatar karin kudin da zai kai naira miliyan 25.