An kashe mutum 5 da kone gidaje 12 a rikicin Jos

Hukumar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da kisan mutum biyar da kone gidaje 12 a rikicin da aka yi ranar  Lahadi. Rikicin ya barke ne a tsakanin matasan Anguwan Damisa da Dutse-Uku bayan ganin gawar wani matashi, rikicin ya shafi wasu yankunan Tina da Anguwan Rukuba duk a karamar hukumar Jos ta Arewa. Jami’in […]

An kashe mutum 5 da kone gidaje 12 a rikicin Jos

Hukumar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da kisan mutum biyar da kone gidaje 12 a rikicin da aka yi ranar  Lahadi.

Rikicin ya barke ne a tsakanin matasan Anguwan Damisa da Dutse-Uku bayan ganin gawar wani matashi, rikicin ya shafi wasu yankunan Tina da Anguwan Rukuba duk a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar  DSP Tyopev Terna, ya tabbatar da aukuwar rikicin ya kuma ce, a yanzu haka gawar na babban asibitin Filato.