An kashe mutum 50 da jami’an JTF a Zamfara- Kakakin majalisa

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Sanusi Rikiji, a yau Juma’a ya ce akalla an kashe mutum 50 harda jami’an tsaron hadin gwiwa na farin kaya (CJTF) ranar Talata a Zamfara Kakakin majalisar ya bayyana hakan ne a ziyarar ta’aziyyar da ya kai masarautar Kaura Namoda a kan arangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaron […]

An kashe mutum 50 da jami’an JTF a Zamfara- Kakakin majalisa

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Sanusi Rikiji, a yau Juma’a ya ce akalla an kashe mutum 50 harda jami’an tsaron hadin gwiwa na farin kaya (CJTF) ranar Talata a Zamfara

Kakakin majalisar ya bayyana hakan ne a ziyarar ta’aziyyar da ya kai masarautar Kaura Namoda a kan arangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaron CJTF da `yan bindigar a unguwannin karamar hukumar Kaura Namoda.

Alhaji Sanusi Rikiji ya kai ziyarar ne tare da wasu jami`an gwamnatin jihar akan irin kalubalen tsaron da jihar ke fuskanta.