An kashe mutum 7 kan zargin maita a Adamawa

An yi wa wasu mutum bakwai kisan gilla kan zargin maita a kauyen Dasin-Bwate da ke Karamar Hukumar Fufore ta Jihar Adamawa. Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Adamawa, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), cewa tuni ta tura masu bincike zuwa kauyen, bayan faruwar lamarin a ranar Talata. An kama uwa tana […]

An kashe mutum 7 kan zargin maita a Adamawa

‘Yan Sanda

An yi wa wasu mutum bakwai kisan gilla kan zargin maita a kauyen Dasin-Bwate da ke Karamar Hukumar Fufore ta Jihar Adamawa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Adamawa, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), cewa tuni ta tura masu bincike zuwa kauyen, bayan faruwar lamarin a ranar Talata.

Mai magana da yawun Rundunar, DSP Suleiman Nguroje, ya ce, “A lokacin da ’yan sanda suka isa, sun tarar duk mutanen garin, har da dagacin kauyen sun tsere. Amma sun samu gawarwakin wasu mutane bakwai a cikin wani gida”, inji shi.

Sai dai ya bayyana cewa kawo yanzu ba a kama kowa ba, sannan ya roki mazauna kauyukan da ke makwabtaka da wurin da su taimaka wa ’yan sanda da muhimman bayanai.