An kashe mutum 9, an kone gidaje a wani sabon rikici a Filato

Rikicin ya barke ne tsakanin kabilun biyu a kan gonaki.

An kashe mutum 9, an kone gidaje a wani sabon rikici a Filato

Akalla mutum tara aka kashe a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke tsakanin kabilar Montol da Taroh a yankin Ponglong da ke Karamar Hukumar Mikang a Jihar Filato.

Shugaban rikon kwarya na Karamar Hukumar, Daniel Kungmi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rikicin ya barke ne tsakanin wasu mutane biyu, wanda daga baya kuma sai da wasu fusatattun matasa suka mayar da lamarin rikici.

A cewar majiyoyi daga yankin, rikicin ya yi sanadin kone gidaje da dukiya mai tarin yawa, sannan wasu da dama sun tsere daga yankin.

Aminiya ta gano rikicin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Asabar, sakamakon rikicin gonaki da ya barke tsakanin kabilun biyu.

Majiyar ta kara da cewa, an jibge jami’an tsaro da yawa a yankin domin tabbatar da zaman lafiya a yanki, yayin da wasu matasa suka sace shanu.

Shugaban Karamar Hukumar ya ce: “A cikin kankanin rikicin ya yi sanadin kone gidaje da dukiyoyin mutane. Wasu bata-gari sun samu damar yi wa mutane sata.

“Bayan samun rikicin muka kira jami’an tsaro, kuma tuni suka garzaya domin tabbatar da tsaro.

“Muna da tabbatar da doka da oda a yankin domin kada rikicin ya shafi wadanda ba su ji ba su gani ba,” in ji shugaban.

Jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya ci tura zuwa lokacin hada wannan rahoton.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta