An kashe mutum biyu tare da sace shanu 200 a gonar tsohon Sakataren Gwamnatin Adamawa
Mutum biyu sun rasa rayukansu a lokacin da barayi suka shiga gonar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Adamawa Cif Kobis Ari Thimnu inda kuma suka sace shanusa 200. Wasu mazauna yankin da abin ya faru sun bayyana wa Aminiya cewa barayin na dauke da manyan bindigogi inda suka yi ta harbi a iska a lokacin da […]
Mutum biyu sun rasa rayukansu a lokacin da barayi suka shiga gonar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Adamawa Cif Kobis Ari Thimnu inda kuma suka sace shanusa 200.
Wasu mazauna yankin da abin ya faru sun bayyana wa Aminiya cewa barayin na dauke da manyan bindigogi inda suka yi ta harbi a iska a lokacin da suke wucewa da shanun.
Satar wadda ta gudana a cikin daren a ranar Larabar makon jiya da misalin karfe 11:00 na dare, ta auku ne a gonar Cif Kobis Ari da ke wajen garin Guyuk inda barayin suka kashe makiyaya biyu suka daure daya.
’Yan sandan Jihar Adamawa sun tabbatar da aukuwar wannan bakin aiki kuma sun ce suna bincike a kai. Sai dai Kakakinsu DSP Othman Abubakar ya ce mutum daya ne ya rasu alokacin satar kuma shanu 36 ne aka sace.