An kashe mutum tara a rikicin Fulani a Bauchi

An kashe mutum tara tare da jikkata wasu shida a rikicin filaye tsakanin al’ummar Fulani a kauyen Zadawa da ke Karamar Hukumar Misau ta jihar Bauchi. Rikicin ya barke ne a sadda jami’an gwamnati suka je fitar iyakar filayen noma da na kiwo a kauyen, bayan bangarorin da ke rikicin sun amince da matakan kawo […]

An kashe mutum tara a rikicin Fulani a Bauchi

An kashe mutum tara a rikicin Fulani a Bauchi

An kashe mutum tara tare da jikkata wasu shida a rikicin filaye tsakanin al’ummar Fulani a kauyen Zadawa da ke Karamar Hukumar Misau ta jihar Bauchi.

Rikicin ya barke ne a sadda jami’an gwamnati suka je fitar iyakar filayen noma da na kiwo a kauyen, bayan bangarorin da ke rikicin sun amince da matakan kawo karshensa, a fadar Sarkin Misau Ahaji Ahmed Suleiman.

“Sun amince jami’an hukumar noma su je su fitar da hanyar dabbodbi a yankin domin kauce wa lalata amfanin gona, amma da suka isa sai wasu futattun matasa dauke da makamai suka dirar musu har suka kashe daya daga cikinsu”, inji Shugaban Karamar Hukumar, Yaro Mohammed Gwaram.

Mazaunan Misau sun ce wasu wadanda ba su yarda a fitar da iyakan ba ne suka tayar da rikicin a lokacin da ma’aikatan suka je su ware wa makiyaya filinsu daban da na manoma, amma matasan suka yi zargin za a mayar da wuraren kiwonsu su koma gonaki.

Da yake tabbatar da abin da ya faru, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na jihar, DSP Ahmed Mohammed Wakili ya ce rikicin ya samo asali ne tsakanin al’ummomin Fulanin kan iyakar da ake kokarin shatawa tsakanin gonaki da wurin kiwon dabbobi.

Amma ya ce jami’an tsaro sun isa kauyen domin tabbatar da kwanciyar hankali da dakile ramuwar gayya tare da kame wadanda ke da hannu domin gurfanar da su a kotu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno