An kashe mutum uku a rikicin girbin amfanin gona

Akalla mutum uku aka kiyasta sun mutu a wani rikici da aka danganta shi da batun girbin amfanin gona a tsakanin al’ummar Beebo da makwabtansu na Okwabang da ke karamar Hukumar Boki a Jihar Kuros Riba, inda kuma aka kona gidaje masu yawa. Binciken Aminiya ya gano cewa a ranar Talatar da ta gabata ce […]

An kashe mutum uku a rikicin girbin amfanin gona

Akalla mutum uku aka kiyasta sun mutu a wani rikici da aka danganta shi da batun girbin amfanin gona a tsakanin al’ummar Beebo da makwabtansu na Okwabang da ke karamar Hukumar Boki a Jihar Kuros Riba, inda kuma aka kona gidaje masu yawa.

Binciken Aminiya ya gano cewa a ranar Talatar da ta gabata ce shugaban matasa Manjok suna sintiri sai suka yi zargin sun ga wani mutumin kauyen Beebo yana girbin amfanin gona na mutumin kauyen Okwabang. Daga nan ne sai cacar baki ta fara, abu kamar wasa har lamari ya kazance, ya kai ga kone-kone da kuma asarar rayuka.

Al’umomin biyu sun shafe shekaru masu yawan gaske suna gwabza fada a tsakaninsu. Kuma kauyuka ne da Allah Ya huwace musu kasar noma, inda bayan noman koko suna noma sauran amfanin gona irin su gero da masara da doya.

Aminiya ta tuntubi Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, Hafiz Muhammad Inuwa, game da lamarin, ya ce mutum uku ne suka rasa rayukansu kuma kura ta lafa, sakamakon tura jami’an tsaro da aka yi; kowa kuma ya koma bakin harkokinsa. Haka kuma ya ce an kama mutum uku da ake zargi da haddasa fitinar, suna nan ana bincike.

Ya zuwa rubuta wannan labari hankali ya kwanta, kowa na ci gaba da yin girbin amfanin gonarsa.