An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden

Ƙone Al-Ƙur’ani da ya yi a 2023 ya haifar da rikici da zanga-zanga a ƙasashen Musulmi.

An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden

An harbe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani, Salwan Momika, ɗan asalin ƙasar Iraƙi mai shekaru 38, a gidansa da ke Södertälje, kusa da birnin Stockholm a Sweden.

A harbe shi lokacin da yake ƙoƙarin wallafa bidiyo a kafar TikTok.

Salwan Momika, ya ƙone Al-Ƙur’ani a 2023 a wajen Babban Masallacin Birnin Stockholm, lamarin da ya jawo cece-ku-ce da zanga-zanga a ƙasashen Musulmi.

Lamarin ya haifar da rikicin diflomasiyya, ciki har da kai hari ofishin jakadancin Sweden da ke Bagdad, da kuma korar jakadan Sweden da ke Iraƙi.

A halin yanzu, ’yan sanda sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan, kuma suna ci gaba da bincike don gano musabbabin harin.