An kashe N2trn kan gyaran lantarki amma kamar an shuka dusa
Ayyukan lantarki guda 334 aka bayar wadanda har yanzu ba a kammala su ba, duk da cewa sun ci sama da Naira tiriliyan biyu
Ayyukan samar da wutar lantarki na sama da Naira tiriliyan biyu ne gwamnati ta bayar a faɗin Najeriya, amma har yanzu kamar an shuka dusa, ba su fara aiki ba.
Matsaloli sun dabaibaye ɓangaren wutar lantarkin Najeriya tsawon shekaru, kuma bisa alamu, matakan da gwamantin ƙasar ta ɗauki shekaru tana aiwatarwa domin magance su sun kasa share wa ’yan ƙasar hawaye.
Masana dai sun yi amanna cewa muddin aka samu tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya mai yawan al’umma mutum miliyan 230, ƙasar za ta samu ci-gaban da ta zaƙu ta samu a ɓangaren masana’antu da samar da ayyukan yi ga ’yan kasarta.
A halin yanzu ƙarfin wutar lantarkin Najeriya migawat 4,500 ne, duk da cewa akwai ayyuka dadan-dadan na sama da Naira tiriliyan biyu da gwamnatin ƙasar ta bayar na gyaran wutar.
- Tukunyar iskar gas ta jikkata mai juna biyu da ’ya’yanta 4 da ma’aurata
- Saudiyya ta sako matan Najeriya da ta tsare kan safarar kwayoyi
- Faɗa da Buratai: Matan ’yan Shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna
Har yanzu dai haƙa ta kasa cim-ma ruwa a ɓangaren, kuma bincikenmu ya gano yawancin ayyukan da aka bayar ba a kammala su ba, musamman na bangaren samarwa da kuma rarraba wutar.
Masana na zargin rufa-rufa da matsalolin gudanarwa da suka yi kaka-gida da rashin bibiya, a matsayin manyan sabubban yin watsi da ayyukan da kuma tafiyar hawainiya da suke yi.
Ana iya tuna cewa a kasafin Najeriya na shekarar 2025 Shugaban Ƙasar, Bola Ahmed Tinubu ya ware Naira tiriliyan 2.09 ga ɓangaren wutar lantarki.
Manyan ayyuakan:
A shekarar 2004 ne Gwamantin Obasanjo ta ƙirƙiro Shirin Samar da Wutar Lantarki na Ƙasa (NIPP) da nufin magance matsalar da inganta kayan aiki da kuma samar da wutar da rabonta a Najeriya.
A lokacin an fara ware wa shirin wanda ake kula da shi daga Asusun Rarar Mai (ECA) kuɗi Dala biliyan 2.5, daga bisani aka ƙara sama da Dala biliyan takwas.
A rukunin farko an ɗora wa NIPP alhakin gina tashoshin lantarki guda 10 masu amfani da iskar gas, wadanda za su samar da wutar da jimillar ƙarfinta ya kai migawat 4,528.5.
An kammala bakwai daga cikin tashoshin, sauran ta Egbema da ke Owerri, a Jihar Imo da kuma ta Gbarain a Jihar Bayelsa. A shekarar 2017 ya kamata a kammala su, amma wasu matsaloli suka sa aka samu jinkirin shekara bakwai yanzu a tashoshin da ake fata za su ba da gudummawa wajen ƙarin ƙarfin wutar ƙasar.
A shekara 2015 aka ƙaddamar da rukuni na biyu na NIPP da nufin gina tashoshin lantarki 16 daga ruwa, waɗanda yawancinsu suke a yankin Arewa, ciki har da Tashar Mambilla, wadda har yanzu suna ce.
Hakazalika an kasa kammala aikin Tashar Kudenda mai ƙarfin 215MW wadda tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya fara. A yanzu dai an ayyana shekarar 2025 ɗin da muka shigo a matsayin sabon lokacin da za a bude ta.
Wani aikin wutar lantarki da aka kasa kammalawa a rukuni na biyun shi ne wanda aka ware wa Dala miliyan 38.7 na haɗin gwiwar Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC) da Kamfanin Mai na Agip (NAOC) a yankin Okpai da ke Ƙaramar Hukumar Ndokwa ta Gabas a Jihar Delta.
A shekarar 2019 aka ba da aikin Tashar Wuta ta Gurara II mai ƙarfin megawat 360 da ke Jihar Kaduna. Duk da cewa Bankin Kasashen Waje na Ƙasar China (Exim) ya amince ya ba wa Najeriya rancen Dala biliyan ɗaya domin aiki, har yanzu ba a kammala ba.
Haka zalika aikin samar da lantarki ta karfin iska mai karfin Migawat 10 a Jihar Katsina yake tafiyar hawainiya. Da farko Gwamantin jihar ce ta ƙirƙiro aikin a shekarar 2005, daga bisani ya koma hannun Gwamantin Tarayya a 2007, amma duk da haka, har yanzu ba a kammala ba, duk da cewa an sa shekarar 2012 a matsayin wa’adin kammala shi.
Dalilai da dama sun hana kammala aiki, ciki har da batun kuɗi, amma a baya-bayan nan gwamnatin jihar ta yi ce za ta sake farfaɗo da shi.
Ayyukan samar da wuta
Bayanan da muka samu daga Kamfanin Samar da Lantarki ta Kasa (TCN) ya nuna ayyukan wutar guda 334 aka bayar daga shekarar 2007, wadanda har yanzu ba a kammala su ba, duk da cewa sun ci Dala biliyan 1.7 da Naira biliyan 125.2 (sama da Naira tiriliyan biyu) daga Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka da Bankin Raya ƙasar Faransa da sauransu.
TCN ya bayar da dalilai masu yawa kan rashin kammala ayyukan. Hukumar Ƙawance Ƙasar Japan (JICA) da Kamfanin Siemens na ƙasa Jamus da Bankin Afirka da Hukumar Raya Kasar Faransa na daga cikin masu ba da kuɗaɗen ayyukan.
Takardun da muka samu daga TCN sun nuna a tsara kammala 34 daga cikin ayyukan a shekarar 2020 da 61 a 2021 sai 21 a 2022 da kuma 180 a 2023 a yayin da ba a ayyana lokacin kammala ragowar 38 ba.
Amma duk da haka, Gwamantin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Kasafi ta Tarayya ta ce har yanzu abin da aka yi bai fi kashi 1% a aikin gina tsahar lantarki ta Kafanchan a Jihar Kaduna ba, wanda aka fara a 2007 da wa’adin kammalawa a watan Disamba 2020.
Rahoton ma’aiakatar ya kara da cewa kuɗin aikin da aka bayar a kan Naira miliyan 72.191 ya ninka fiye da sau uku, zuwa miliyan N277.22.
Sauran ayyukan
Wasu daga cikin manyan ayyukan da aka bayar sun haɗa da tashar Ikorodu-Odogunyan-Shagamu 132kV DC wanda aka bayar a watan Disamaban 2009; Ƙaramar Tasahar Nnewi 2×60 MVA 132kV a Jihar Anambra a 2006; 2x330KV line bay a Kaduna, Jos da Onitsha, a watan Nuwamba da kuma na Kano-Katsina 330KV DC.
Sauran su ne ƙaramar tasha mai ƙarfin 2x60MVA, 132/33kV a Malumfashi, Jihar Katsina wanda aka bayar a 2011; da ƙaramar tashar 2x60MVA, 132/33kV a Aboh Mbaise da kuma 2x132KV line bays extension a Owerri, Jihar Imo a shekarar 2009; da kuma tashar 2x60MVA,132/33KV a Mpu, da kuma 2x132kV line bay extension a Nnewi, Jihar Enugu; 2X60MVA substation a Ede, Jihar Osun; karamar tashar 2x 60MVA 132/33KV a Egbe da kuma 2x132KV line bays a Omu-aran da ke Jihar Kogi da dai sauransu.
Siyasa ce ta sa aka kirkiro ayyukan —Minista
Amma daraktan yaɗa labaran ma’aikatar, Florence Dibiaezue-Eke, ta ce ba ta da masaniya kan ayyukan da ba a kammala ba a karkashin kulawar ma’aikatar, amma za ta tuntubi daraktan da ke kula da ayyuka domin samun karin bayani.
A bara ne Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce siyasa ce ta sa gwamnatocin baya suka ƙirƙiro wasu daga cikin ayyukan lantarki da ba a kammala ba a fadin kasar nan.
“An kashe kuɗaɗen gwamnati dai kawai amma babu amfanin da aka samu. Ba ma cin gajiyar ayyuakan. Ni a lokacina ba zan lamunci hakan ba,” in ji shi.
Ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar za ta yi bakin ƙoƙari domin kammala sama da ayyuka 100 da aka yi watsi da su, domin inganta samar da wutar lantarki a ƙasar.