An kashe Na’ibin Shekau a musayar wuta da sojoji – Hedkwatar Soja

Hedkwatar Sojan Najeriya ta ba da sanarwar mutuwar wani mai suna Momodu Bama da aka ce shi ne Na’ibin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau. Wata sanarwa daga Daraktan Labarai na Sojan Najeriya Birgediya Janar Chris Olukolade, ta fadi a shekaranjiya Laraba cewa, “A yayin da sojoji suka kara himmar farautar ’yan ta’adda da suke […]

An kashe Na’ibin Shekau a musayar wuta da sojoji – Hedkwatar Soja

 Admiral Ola Sa’ad Ibrahim Babban Hafsan TsaroHedkwatar Sojan Najeriya ta ba da sanarwar mutuwar wani mai suna Momodu Bama da aka ce shi ne Na’ibin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.
Wata sanarwa daga Daraktan Labarai na Sojan Najeriya Birgediya Janar Chris Olukolade, ta fadi a shekaranjiya Laraba cewa, “A yayin da sojoji suka kara himmar farautar ’yan ta’adda da suke halaka jama’a a jihohin Borno da Yobe, sauran ’yan ta’addan da aka kama sun tabbatar da mutuwar Na’ibin shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Wannan ya biyo bayan fafatawa da soja suka yi da ’yan ta’adda a yankin Bama. Momodu da kansa yake jagorantar kai hare-hare ga sojoji da sauran jama’ar da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a Yobe da Adamawa.”
Sanarwar ta ce, “Wani kwararre ne wajen sarrafa bindigogin harbor jiragen sama na kungiyar, kuma ya yi fice wajen tsaurin rai da rashin tausayi, inda da hannunsa yake yanka mutanen da suka shiga hannunsa.”
“Momodu Bama yana daga cikin wadanda ake nema kan ayyukan ta’addanci, inda aka ajiye ladar Naira miliyan 25 kan duk wanda ya fallasa inda za a same shi,” inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Sauran wadanda suka mutu a fafatawar sun hada da mahaifin Bama Alhaji Abatcha Filatari, wanda malami ne ga haramtacciyar kungiyar. Sai kuma wasu mutum 17 da suka rasu a fafatawar, yayin da mutum 24 suka shiga hannu.”
Kashe Na’ibin na Shekau ya zo ne kasa da mako daya da ’yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka halaka akalla mutum 52 a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata a wasu kauyuka na kananan hukumomin Mafa da Konduga da ke Jihar Borno.
Wakilanmu sun ce a kauyen Ngom da ke iyakar Mafa da Konduga kan hanyar Gamboru-Ngala, maharan sun yanka mutum 12 cikin dare a ranar Asabar, yayin da suka yi yankan rago ga mutum 40 a kauyukan Mandarari da Malari a karamar Hukumar Konduga a hanyar Maiduguri zuwa Bama.
Bayanai sun ce maharan suna sanye ne da kayan soja da na ’yan sanda inda suka kai hare-hare kauyukan cikin motoci hudu. Shaidu sun ce mutane da dama sun samu raunuka a yayin harin, kuma maharan sun banka wa gidaje da dama wuta a kauyukan.
Wata majiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ta tabbatar da cewa mutum 26 da suka samu raunuka sauna jinya a asibitin. “Jami’an JTF sun kawo su nan (asibitin) a motoci uku don yi musu jinya. Goma sha shida daga cikinsu sun samu karaya a hannuwansu, yayin da saura suke dauke da raunukan yankar wuka da kuna,” inji wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta.  
daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya yayin harin kauyen Ngom ya ce: “Wasu daga cikinmu sun tsira ne ta hanyar fadawa cikin daji da gudu.” Ya ce, sun samu bayani daga baya cewa maharan sun dauki fansa ne kan abin da suka kira hadin kan da mutanen kauyen ke ba jami’an tsaro.
Jami’an JTF ba su tabbatar da yawan mutanen da suka halaka ko aka raunata zuwa lokacin hada wannan rahoto ba, amma wani dan siyasa daga Mafa ya tabbatar da halaka mutum 12 a yankin, inda ya ce sun samu labarin harin da aka kai Konduga ya ci mutum 40.
A wani labarin kuma jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani faifai a ranar Litinin da ta gabata inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da sojoji da kin bayyana hakikanin al’amura ga jama’a kan hare-haren da ke gudana a yanzu, inda ya ce har yanzu yana nan da rai.
Shekau wanda ya yi magana da Hausa da Larabci a faifansa mai taken Goron Sallah ya dauki nauyin kai hare-hare a garuruwan Malam Fatori da Bama da kuma Gamboru-Ngala a makonni biyu da suka gabata, inda aka halaka wasu jami’an tsaro. Kuma ya ce shi da mayakansa za su ci gaba da yaki har karshen rayuwarsu, kuma ya shaida wa matasa ’yan sa-kai su daina bata lokacinsu wajen farautar mambobinsa.