An kashe rai an harbi wasu 6 a rikicin sojoji da matasa a Bauchi

An ji wa mutane shida raunukan harbi an ƙone fadar hakimin garin Lere a rikicin

An kashe rai an harbi wasu 6 a rikicin sojoji da matasa a Bauchi

’Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a rikicin da ya ɓarke tsakanin sojoji da matasa a garin Lere da ke Ƙaramar Hukumar Tafawa Ɓalewa a Jihar Bauchi.

Shaidu sun ce bayan wanda aka kashen, an ji wa mutane shida raunukan harbi a sakamakon samamen da sojojin suka kai cikin gidaje da kuma kan matasan Jam’iyyar PDP da suka yi faɗa da su.

Rundunar ’yan sandan jihar ta bayyana cewa sojojin rundunar Operation Safe Haven sun ba hamata iska da matasan Jam’iyyar PDP ne a wani shingen bincike da ke garin.

Kakakin rundunar, SP Ahmed Walil, ya ce, “tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Auwal Musa Mohammed, ya tura ƙarin  jami’an kwantar da tarzoma zuwa yankin.

“A halin da ake ciki kuma, an fara gudanar da bincike domin gano gaskiya da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi.”

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya da raunin harbi a rikicin, Babawo Lauwawu, ya ce rikicin ya samo asali ne daga ƙoƙarin sojojin na aiwatar da dokar hana fita da suka ƙaƙaba a garin na Lere.

“Mun fito daga teburin mai shayi sai muka ji cewa an sanya dokar hana fita kuma za ta fara aiki ne daga ƙarfe 10 a daren jiya (Talata).

“Ba mu san wanda ya sa dokar ba, amma duk da haka muka yi biyayya muka shige gida tun karfe 9, kafin lokacin dokar ya yi.

“Da misalin ƙarfe taran, kafin dokar ta fara aiki ne kuma muka fara jin harbe-harben jami’an tsaro daga cikin gidajenmu.

“A sakamakon harbi kan mai uwa da wabi da suke yi har suka same ni harsashi a ƙafata.

“Mu dai ba mu san dalilin harbe-harben nasu ba,” in ji Babawo.

Shi ma wani da aka harba a yayin rikicin, Zaharadden Mohammed, ya ce, ana zargin sarkin (Hakimi) garin ne ya buƙaci sojoji su sanya dokar hana fitar daga ƙarfe 10 na dare.

Zaharadden ya ce hakan ya faru ne bayan rikici a wani shingen bincike tsakanin sojojin da wasu mambobin Jan’iyyar PDP da suka dawo daga yaƙin neman zaben ƙananan hukumomi da ke tafe.

Ya ce, “Matasa ne suka yi faɗa da sojoji, sakamakon haka sojojin suka yanke shawarar amfani da dokar hana fitar domin far wa abokan faɗan nasu.

“Tun da misalin ƙarfe 9 na dare kafin dokar ta fara aiki sojoji suka ƙaddamar da samamen nasu.

“Bayan harbe-harben sun lafa, sai aka kira mu zuwa fadar sarki cewa mu je mu saurari jawabin shugaban ƙaramar hukumarmu.

“Muna cikin jiran isowan ciyaman din ne, shugaban matasa ya buƙaci wani ɗan tauri da ke aiki da sojojin, ya dakatar da harbin da yake yi, amma ɗan taurin ya ƙi.

“Kafin mu ankara, ɗan taurin nan ya sa bakin bindigarsa a fuskata, ya harba, ya fasa min ido ɗaya, yanzu ba na gani sai da ido ɗaya.

Bayan wayewar garin ranar Laraba, fusatattun matasa suka ƙone fadar Hakimin Lere, Alhaji Jamilu Aliyu Bawa, kan harbin matasan da kuma sanya dokar hana fitar.

Wakikinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin hakimin garin da ake zargi, amma abin ya faskara, zuwa lokacin da aka kammala wannan labarin.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS