An kashe sabon ango a harin da aka kai kasuwa a Neja
Harin na zuwa ne yayin da a bayan nan rundunar ’yan sandan jihar ta hana ’yan banga ayyukan inganta tsaro da suke yi a yankin.
’Yan bindiga sun harbe wani sabon ango yayin harin da suka ƙaddamar a kasuwar Madaka da ke Karamar Hukumar Rafi a Jihar Neja.
Angon wanda aka bayyana sunansa da Sani, na daga cikin mutum 21 da ’yan bindigar suka hallaka a kasuwar da manoma ke ci mako-mako a ranar Alhamis.
Bayanai sun ce angon wanda mahauci ne da ke zaune a garin Kagara na Karamar Hukumar Rafi, ya fita kasuwar ce inda yake sana’ar sayar da nama lokacin da harin ya auku.
- ’Yan bindiga sun hallaka gomman mutane a Neja
- ’Yan bindiga sun kone gidaje 30, shanu 100 da kayan abinci a Neja
Kazalika, ’yan bindigar da suka kai harin da tsakar rana sun tilasta wa mata musulmi karya azuminsu.
Mazauna yankin sun ce an ƙaddamar da harin ne da misalin ƙarfe 3 na yammacin ranar Alhamis lokacin da hada-hada a kasuwar ta ɗauki harama.
Wani mazaunin yankin mai suna Salihu Abdullahi, ya bayyana cewa ’yarsa mai kimanin shekaru takwas na cikin waɗanda ’yan bindigar suka harbe.
Da yake zantawa da Aminiya a Asibitin ƙwararru na IBB inda aka kai ’yarsa da aka harbe, ya ce ‘yan bindiga sun tilasta wa matan da lamarin da rutsa da su da su karya azuminsu ko kuma a bakin rayukansu.
“Muna ƙauyen da ke maƙwabtaka da mu inda muka je wurin haƙo zinare sai muka ga mutane suna gudu.
“Wasu mutane sun riƙa faɗawa cikin kogin, har ma da waɗanda ba su iya ruwa ba. Don haka, na yi yunƙurin garzayawa gida a kan babur ɗina don ɗaukar iyalina.
“A kan hanya aka tsayar da ni cewa gwara na koma domin kuwa ’yan bindigar sun riga sun mamaye unguwannin.
“Sun ƙona asibitinmu da shagunan da ke ɗauke da kayayyaki na miliyoyin naira, babura, manyan motoci, kayan abinci da gidaje.
“Sun tara matanmu sun tilasta musu karya azumin da suke yi.
“’Yata ƙarama mai shekara takwas na cikin waɗanda suka harbe.
“Da farko an ƙirga gawarwaki 11 amma daga baya aka sake gano wasu gawarwakin.
“Kuma har ya zuwa yanzu, akwai mutane da dama da muka nema muka rasa
“Akwai kuma waɗanda da dama sun tsere cikin daji da raunukan harsashi watakila sai dai a tsinto a gawarsu.
“A tsawon shekaru, ‘yan banga sun kare al’ummarmu. Muna ba da gudummawar kuɗi don biyan su kuma muna saya musu kayan abinci domin ƙara musu ƙaimin fuskantar aikin tsaro da inganci.
“Tun da muka kafa kungiyar ’yan banga, ‘yan bindiga ba su kai wa al’ummarmu hari ba.
“Sai dai ba mu san abin da ke faruwa ba domin a bayan nan ’yan sanda suka zo suka tafi da kwamandan ’yan bangar tare da ba su umarnin daina aiki.”
Mazauna yankin dai na zargin cewa ‘yan bindiga sun mamaye unguwar mako guda bayan da jami’an ‘yan sanda suka cafke kwamandan ‘yan banga.
Haka kuma, sun ce harin na zuwa ne bayan an umarci ’yan bangar da su daina gudanar da ayyukan da suke yi bisa zarginsu da kamen makiyaya da suka yi ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaban matasan Madaka, Saidu Bwale, ya yi zargin cewa harin na ranar Alhamis na ɗaya daga cikin mafi muni da aka kai wa unguwar.