An kashe shahararren matsafi a Osun
Wasu rukunin matsafa sun kashe shahararren matsafin da aka fi sani da suna Badoo da ke zaune a Osogbo babban birnin jihar Osun. An dai kashe Badoo ne a wata mashaya da aka fi sani da ‘Star Night’ kusa da tsohuwar sakatariyar APC a unguwar Ladsol Osogbo lokacin da aka samu rashin jituwa tsakanin rukuni […]
Wasu rukunin matsafa sun kashe shahararren matsafin da aka fi sani da suna Badoo da ke zaune a Osogbo babban birnin jihar Osun.
An dai kashe Badoo ne a wata mashaya da aka fi sani da ‘Star Night’ kusa da tsohuwar sakatariyar APC a unguwar Ladsol Osogbo lokacin da aka samu rashin jituwa tsakanin rukuni biyu na matsafan.
Hukumar ‘yan sandan jihar ta shiga tsakanin rukunin matsafa don kauce wa yaduwar rikicin a wasu yankunan jihar.