An kashe shi a kan bashin kudin kayan maye
A ranar Talatar makon jiya ne wani matashi ya kashe abokin cinikinsa a Unguwar dorayi Ciranci da ke karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano sakamkon kasa biyansa kudin maganin tari da matasa ki amfani da shi wajen maye. Binciken Aminiya ya gano cewa matashin mai suna Abdul’aziz Shehu Adamu ya gamu da ajalinsa ne saboda […]
A ranar Talatar makon jiya ne wani matashi ya kashe abokin cinikinsa a Unguwar dorayi Ciranci da ke karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano sakamkon kasa biyansa kudin maganin tari da matasa ki amfani da shi wajen maye.
Binciken Aminiya ya gano cewa matashin mai suna Abdul’aziz Shehu Adamu ya gamu da ajalinsa ne saboda ya gaza biyan bashin kudin sirop na Naira 1,200 da wani abokin huldarsa mai suna Sanusi dan Koc ke bin sa.
Wani ganau da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa rikicin ya samo asali ne a lokacin da Sanusi ya nemi kudinsa daga wurin marigayin wanda ya gaza biya. “Abdul’aziz ya karbi bashin sirop daga wurin Sanusi to ran nan sai ya nemi kudinsa, shi
kuma ya nuna ba ya da kudi. Daga nan ne sai rigima ta kaure a tsakaninsu, ba a yi aune ba sai Sanusi ya zaro wuka ya burma a cikin Abdul’aziz, inda aka dauke shi zuwa Asibitin Murtala inda rai ya yi halinsa,” inji shi.
Hajiya Mama dorayi mahaifiyar Abdul’aziz ta shaida wa Aminiya cewa ba ta gida lokacin da abin ya faru sai waya aka yi aka sanar da ita halin da danta yake ciki. “Ba na nan sai wasu yara suka kira ni suka gaya min cewa ga shi wani ya burma wa Abdul’aziz
wuka a ciki, an dauke shi zuwa asibiti. Nan take na wuce asibitin don sanin halin da ake ciki a nan ne kuma na tarar da shi har ya cika,” ta fadi cikin kuka.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wanda ake zargin da aikata laifin wato Sanusi dan Koc ya gudu. Sai dai Majiya ya ce rundunarsu za ta yi kokarin ganin wanda ake zargin ya zo hannu don fuskantar hukunci.