An kashe shugaban cibiyar horar da nakasassu ta Abuja

Kawo yanzu ba a san waɗanda suka kashe shugaban cibiyar ba.

An kashe shugaban cibiyar horar da nakasassu ta Abuja

Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Abuja

Wasu da ba a san ko su wane ba, sun kashe Shugaban Cibiyar Bai Wa Nakasassu Horo da ke, Abuja, Kwamred Bala Tsoho Musa.

An kashe marigayin ne a ranar Juma’a a kofar gidansa da ke cikin cibiyar a ƙauyen Kuchiko a bayan garin Bwari a Abuja.

Wasu mazauna garin da Aminiya, ta zanta da su ta waya a ranar Asabar sun bayyana cewa, an tarar da gawar marigayin a gaban gidansa kusa da kekensa na guragu.

Har wa yau, an ga wani katako da a ke zargin an yi amfani da shi wajen dukansa a kai, wanda aka masa rauni.

“Babu wani daga cikin gidansa da ya sa lamarin ya faru, watakila saboda ƙarar janareta da ke kunne a gidan, har sai da wata kurma da ke zuwa gidansa ta ke taya iyalansa aiki ta fita da nufin komawa makwancinta da ke ɓangaren kamammun mata,” in ji majiyar.

Ɗaya daga cikin waɗanda wakilinmu ya zanta da su ya ce ba samu wayoyin marigayin guda biyu a tare da shi ba, wanda hakan ke nuna cewa an gudu da su.

Bayanai sun nuna marigayin kan zauna a kofar gidansa na wani lokaci da daddare bayan yin kewayen cibiyar, kafin ya koma gida.

Babban jami’in ’yan sanda na Bwari, CSP Babayola Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin.