An kashe Shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran
An kashe Ismail Haniyeh bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran
An hallaka shugaban kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh a safiyar Laraba a lokacin ziyarar da ya kai kasar Iran.
Kungiyar Hamas ce ta sanar da hakan, tana mai zargin Isra’ila da wannan kisa jim kadan bayan ya halarci taron bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran.
Babban jami’in Hamas, Sami Abu Zuhri, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, “Isra’ila ce ta kashe Dan Uwa Ismail Haniyeh da nufin karya lagon Hamas.”
Kisan Ismail Haniyeh dai ya haifar da fargabar yiwuwar hargitsewar yakin Isra’ila da kungiyar a Zirin Gaza da kuma Hezbollah a kasar Lebanon.
- Ba a ba mu abincin tallafi ba —Gwamnatin Adamawa
- ’Yan bindiga 31 sun shiga hannu a Nasarawa
- Ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi
Labarin kisan Ismail Haniyeh na zuwa ne kimanin awa 24 bayan Isra’ila ta yi ikirarin kashe wani kwamandan kungiyar Hezbollah a Tuddan Golan.
Rundunar Juyin Juya Halin Iran ta tabbatar da labarin kisan Ismail Haniyeh a kasar.
Rundunar ta bayyana cewa tana gudanar a bincike kan lamarin, amma kawo yanzu babu wani martani daga Isra’ila kan kisan na shugaban Hamas, Ismail Haniyeh.
Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas, ya la’anci kisan, a yayin da bangarorin kasar da ke yankin yammacin Kogin Jordan suke kira da a gudanar yajin aiki da zanga-zangar gama-gari.
Isra’ila ta sanar cewa tana gudanar da bincike kan kisan na Ismail Haniyeh, amma ba ta fitar da wani sakon gargadi ga fararen hulanta ba.