An kashe Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa a Mali

Lamarin ya faru ne a kauyen Nara da ke lardin Koulikoro da ke Kudu maso Yammacin kasar.

An kashe Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa a Mali

A kasar Mali an hallaka wasu manyan jami’an gwamnati biyar na kusa da Shugaban rikon gwamnatin kasar, Kanal Assimi Goita.

Rahotanni daga Bamako babban birnin kasar, sun ruwaito cewa wani harin kwantar bauna ya hallaka Oumar Traore, Shugaban Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa da wasu jami’an gwamnati hudu yayin da direban tawagar ya bata.

Kafar watsa labarai ta Aljazeera ta ruwaito cewa,  lamarin ya faru ne a kauyen Nara da ke lardin Koulikoro da ke Kudu maso Yammacin kasar.

Kawo yanzu dai babu tabbacin wadanda ke da alhakin harin, amma kuma kasar Mali a yanzu kusan ita ce kan gaba wajen fama da tarzomar ’yan ta’adda a Yammacin Afirka.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50