An kashe sojoji 16 da ’yan Boko Haram 150 a Borno
Sojoji 16 da ’yan Boko Haram 150 ne suka mutu a wata fafatawa da bangarorin biyu suka yi lokacin wani farmaki da sojojin suka kai dajin Kafiya da ke tsakanin Maiduguri da Bama da ke Arewacin Jihar Borno.Kakakin Sojojin Najeriya Birgediya Janar Ibrahim Attahiru ne ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata, inda […]
Sojoji 16 da ’yan Boko Haram 150 ne suka mutu a wata fafatawa da bangarorin biyu suka yi lokacin wani farmaki da sojojin suka kai dajin Kafiya da ke tsakanin Maiduguri da Bama da ke Arewacin Jihar Borno.
Kakakin Sojojin Najeriya Birgediya Janar Ibrahim Attahiru ne ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce sojoji tara sun bace a lokacin fafatawar, kuma har zuwa lokacin ba a gano su ba.
Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis din makon jiya, amma sai a ranar Talatar mahukunta suka tabbatar da mutanen da suka mutu, bayan da wata kafar labarai ta intanet ta fadi adadi mai yawa na wadanda suka mutu.
Sanarwar farko daga Runduna ta Bakwai a ranar Asabar ta ce, an kashe mahara “da dama,” amma ba ta ambaci na bangaren soja ba. Sai dai Birgediya Janar Attahiru ya shaida wa Aminiya cewa a ranar 12 ga Satumba, sojoji daga Runduna ta Bakwai da ke Maiduguri sun kai farmaki ga sansanin ’yan Boko Haram da ke dajin. “Kuma a yayin farmakin mun kashe mahara 150, kuma mun rasa sojoji 15, sannan sojoji tara sun bace,” inji shi.
Janar Ibrahim ya ce a yayin fafatawar an kashe wani Kwamandan Boko Haram mai suna Abba Goroma, da aka ajiye ladar Naira miliyan 10 kan duk wanda ya fallasa inda za a kama shi.Ya ce, an iske sansanin dauke da makaman lalata tankunan yaki da na harbo jirgin sama da aka kintsa su a kan motoci.
Kakakin Sojojin ya musanta rahoton da aka bayar a intanet cewa sama da sojoji 40 aka kashe, kuma 65 sun bace bayan da ’yan bindiga suka yi musu kwanton-bauna. Hukumomi sun sha musanta yawan sojojin da suke mutuwa a yayin fafatawa da maharan.
A watan Agusta ’yan Boko Haram sun kai harin da ya halaka sojoji 12 a Malam Fatori da ke Jihar Borno, daga farko sojojin sun ce soja biyu kawai aka kashe, amma daga baya kwamandansu ya tabbatar sojojin da suka mutu sun kai 12.
Wannan shi ne harin da aka fi rasa rayuka da aka bayyana ga jama’a tun sanya dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa a watan Mayu.
A ranar Asabar Kakakin Runduna ta Bakwai Laftana Kanar Sagir Musa ya ce sojoji sun ceto kauyuka uku da ’yan Boko Haram suka mamaye na sama da shekara biyu. Kuma ya ce, suna gudanar da aiki a kauyukan Felo da Gwaoi da kuma Malagara, da ke kananan hukumomin Gubio da Nganzai domin farautar ’yan ta’adda.