An kashe sojojin Nijar 6 da ’yan ta’adda 10 a Tillaberi

Sojojin Nijar sun hallaka masu iƙirarin jihadi 10 a garin Sanam da ke yanki Tillaberi

An kashe sojojin Nijar 6 da ’yan ta’adda 10 a Tillaberi

Nijar (AFP)

Sojojin Jamhuriyar Nijar shida sun rasu a wani harin kwanton ɓauna da mayaƙa masu iƙirarin jihadi suka kai musu a ranar Lahadi.
Gwamnatin sojin Nijar ta ce a yayin musayar wutar, dakarun nata sun hallaka 10 daga cikin a mayaƙan da suka kawo musu farmakin a kan babura a garin Sanam da ke Jihar Tillaberi.
Sabuwar gwamnatin sojin ta ƙara da cewa a ranar 9 ga watan nan na Agusta, ’yan ta’adda sun kashe sojoji biyar a garin na Saman da ke iyaka da ƙasashen Burkina Faso da kuma Mali da suke fama da hare-haren ta’addancin masu iƙirarin jihadi.

Shugaban gwamnatin sojin, Janar  Abdourahamane Tchiani dai ya bayyana cewa sun yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli ne saboda taɓarbarewar sha’anin tsaro a ƙasar.