An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji

An tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji bayan an yi musu kisan gilla

An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji

Gawa

Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra.

Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki.

Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a bude ba yadda suka saba ba, kasancewar yaran suka kulle gidan a duk lokacin da za su je wasa.

Da shigarma’auratan cikin gidan ne kuma suka ga gawarwakin yaran an sanya a cikin firinjin kayan kankara.

Lamarin da ya faru a karshen mako ya tayar da kura, musamman a kafofin sada zumunta.

Bayan hakan ne gwamnatin jihar ta yi alkawarin bin diddigi tare da kama masu hannu a wannan aika-aika.

A yayin ziyarar da ta kai wurin, Kwamishinar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a, Misis Ify Obinabo, ta ba da tabbacin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an yi wa yaran adalci.

Kwamishinar, ta kuma jaddada haka a lokacin da ta ziyarci Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Nnewi, inda aka ajiye gawarwakin yaran.

Mazauna unguwar sun bayyana lamarin a matsayin babban tashin hankali a yayin da suke ta tausaya wa ma’auratan.

Tuni dai hukumomin jihar Anambra suka kaddamar da bincike kan lamarin da nufi lalubo bakin zaren.