An kashe wanda ya kitsa harin Jami’ar Garissa
Hukumomi a kasar Somaliya sun ce an kashe mutumin da ya jagoranci harin da aka kaddamar a Jami’ar Garissa da ke kasar Kenya a shekarar 2015.A baya dama, gwamnatin Kenya ta sanar da sunan Mohamed Kuno a matsayin wanda ya kitsa harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 148, kamar yadda BBC ta bayyana.Dakarun soji […]

Hukumomi a kasar Somaliya sun ce an kashe mutumin da ya jagoranci harin da aka kaddamar a Jami’ar Garissa da ke kasar Kenya a shekarar 2015.
A baya dama, gwamnatin Kenya ta sanar da sunan Mohamed Kuno a matsayin wanda ya kitsa harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 148, kamar yadda BBC ta bayyana.
Dakarun soji na yankin da ke aiki a Somaliya sun ce Kuno, daya ne daga cikin mutane 16 da aka kashe lokacin wani samame a garin Kismayo, da ke kudancin kasar.
Rahotanni sun ce hudu daga cikin wadanda aka kashe manyan mayakan kungiyar al-Shabab ne.
A ranar Laraba ne Ministan Tsaro na yankin Jubaland a Somaliya Abdirashid Janan, ya tabbatar da labarin a wurin wani taron manema labarai.
Bayan harin na Garissa, gwamnatin Kenya ta sanya ladan Dala dubu 215 ga duk wanda ya taimaka aka kama Kuno.
Kuno dan Kenya ne wanda ke da asali a Somaliya, kuma a baya shugaban wata makarantar Islamiyya ce a Garissa har zuwa shekarar 2007.
Daga nan ne ya tsallaka kan iyaka zuwa Somaliya domin shiga kungiyar mayakan Islama ta Union of Islamic Courts (UIC), wacce a wani lokaci a baya take rike da ikon galibin kasar.
Bayan da kungiyar ta UIC ta rushe ne kuma ya shiga kungiyar Hizbul Islam, wacce ta hade kungiyar al-Shabab a shekarar 2010.