An kashe wani Ardo a Abuja
Wasu mahara da ake zargin adadinsu ya kai goma, sun kashe Ardon Fulanin Bwari a yankin Birnin Tarayya Abuja, bayan sun auka gidansa cikin dare ranar Litinin da ta gabata a Baran-Gwani a garin Bwari. Marigayi Alhaji Adamu Dauji da ke rike da Ardon Fulanin Bwari a bangaren Esu Bwari, sama da shekara 20, ya […]
Wasu mahara da ake zargin adadinsu ya kai goma, sun kashe Ardon Fulanin Bwari a yankin Birnin Tarayya Abuja, bayan sun auka gidansa cikin dare ranar Litinin da ta gabata a Baran-Gwani a garin Bwari.
Marigayi Alhaji Adamu Dauji da ke rike da Ardon Fulanin Bwari a bangaren Esu Bwari, sama da shekara 20, ya gamu da ajalinsa ne sa’o’i kadan bayan ya halarci wani taron Fulani daga jihohin kasar nan da ya gudana a wani otel da ke Abuja.
dan uwan marigayin Alhaji Usman Dauji ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da maharan suka kutso gidan da misalin karfe 9:30 na dare sun garzaya zuwa bukkar marigayin kai-tsaye sannan suka bukaci ya bude musu kofa bayan sun ce sun zo gidan ne don su kashe shi. Ya ce bayan ya ki bude kofar, maharan sun yi amfani da bindiga wajen balle kofar sannan suka harbe shi tare da sararsa a wuya, inda suka gudu cikin hanzari.
daya daga cikin matan marigayin, Malama Harira, ta ce mijinta ya kwanta da wuri a daren, sannan sauran iyalansa suka ci gaba da hira daga waje. Ta ce a lokacin da suke hirar wani yaro ya zo gidan ya sanar da su cewa, ya ga wasu da ba a saba gani ba na ta kai kawo a makarantar firamare ta makiyaya da ba ta nisa da gidan. Ta ce, sun sanar da mai gidan nasu al’amarin, inda ya ce kada su da mu Allah zai magance musu komai.
Ta ce bayan kamar minti 30 da zuwan labarin, sai suka fara ganin hasken tocila barkatai an nufo gidansu, kuma a lokacin ne suka ruga daji, inda daga can suka rika jin hayaniyar mutanen a gidansu tare da karar bindiga.
Ta ce daya daga cikin ’ya’yan marigayin mai suna Umaru wanda ke gidan tare da yunkurin fuskantar maharan, ya tsira da rauni a kai, kuma an garzaya da shi asibiti don yi masa magani. Marigayin ya rasu ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 18.
Shugaban ’yan sandan Bwari (DPO) wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce bayan samun labarin, ya ziyarci iyalan marigayin da tawagarsa, inda suka dauki bayanai.