An Kashe Wani Matashi A Hanyar Tafiya Buɗa Baki A Bauchi
Matasan sun samu rashin jituwa ne tsakaninsu, sakamakon haka ɗaya ya zaro wuƙa mai kaifi ya lallaba ta baya daba wa ɗayan.
Wani matashi mai shekara 25 ya rasa ransa a yankin Magama-Gumau na Karamar Hukumar Toro da ke jihar Bauchi sakamakon caka masa wuka a wuyansa.
Khalid Ibrahim ya gamu da ajalinsa ne da yammacin ranar Talata a kan hanyarsu ta tafiya masallaci buɗa baki tare da abokansa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin.
ASP Wakil ya ce “Rundunarmu ta samu rahoton kisan gillar da ya faru a Gumau kuma an tabbatar da cewa Usman Ibrahim, mai shekaru 18 ake zargin ya caka wa Khalid Ibrahim mai shekara 25 wuka a wuya.”
- Muhammad Elsayed Ali Muhammad: Bamisiren da ke nazartar jaridun Hausa
- Tinubu Ya Karrama Sojojin Da Aka Kashe A Delta
Wakil ya bayyana cewa, “matasan sun samu rashin jituwa ne tsakaninsu, sakamakon haka Usman Ibrahim ya zaro wuƙa mai kaifi ya lallaba ta baya daba wa Khalid Ibrahim, inda ya yi masa mummunan rauni, kuma rai ya yi halinsa
“Wanda a dalilin haka sauran matasan da ke tare da su suka ranta a na kare.
“Bayan samun rahoton, rundunar ‘yan sanda karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda, Auwal Musa Mohammed, ta bayar da umarni ga DPO na reshen Toro da su gaggauta zuwa wurin.
“Da zuwan ’yan sanda suka ɗauki wanda abin ya shafa aka garzaya da shi babban asibitin Toro domin duba lafiyarsa.
“Sai dai da isa asibitin, likitoci suka tabbatar da mutuwarsa. Kuma tuni muka miƙa gawarsa ga makusantansa domin su binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.”
ASP Wakil ya bayyana cewa, kwamishinan ’yan sandan jihar ya ba DPO Toro umarnin gabatar da bincike cikin gaggawa.
Ya kuma buƙaci a bayyana wa jama’a gaskiyar abin da bincike ya tabbatar.