An kashe wani mutum a rikicin APC da PDP a Jigawa
Mutum daya ya rasa ransa sakamakon arangamar da magoya bayan jam’iyyun biyu suka yi da juna.
‘Yan sanda
Akalla mutum daya ne ya rasa ransa, wasu biyar kuma suka jikkata bayan wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar PDP da na APC a Jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne a lokacin da dan takarar gwamnan jihar na PDP, Mustafa Sule Lamido, ya gudanar da yakin neman zabensa a Karamar Hukumar Maigatari ranar Juma’a.
- ’Yan sanda sun cafke ’yan banga`r siyasa 93 a Kano
- Canjin Kudi: Buhari ya yi gum bayan cikar wa’adin da ya ba gwamnoni
Rahotanni sun ce bayan isarsu Sakatariyar Jam’iyyar APC, rikici ya barke tsakaninsu da magoya bayan APC.
A cewar sanarwar da ’yan sandan suka fitar, magoya bayan PDP ne suka kai wa wani matashi mai suna Abdullahi Isiyaku, mai shekara 37 da ke zaune a garin Gangare a Maigatari, hari.
An garzaya da shi Babban Asibitin Gumel domin yi masa magani amma daga baya ya mutu sakamakon raunin da ya samu.”
Sanarwar ta kara da cewa, ana gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Dutse.
Kakakin rundunar , DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce ’yan sanda na bincike domin ganin an gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Lamarin da ya haifar da fargaba da tsoro a zukatan mazauna yankin.