An kashe wani mutum a sabon hari a Kudancin Kaduna

An kashe mutum daya tare da jikkata wani mutum guda a wani harin da ba a san ko su wa su ka kai ba a garin Asso da ke karamar hukumar Jama’a da ke shiyyar kudancin Kaduna a ranar Talata da daddare. Wani da ke garin da abin ya faru ya shaidawa Aminiya bayan ya […]

An kashe wani mutum a sabon hari a Kudancin Kaduna

An kashe mutum daya tare da jikkata wani mutum guda a wani harin da ba a san ko su wa su ka kai ba a garin Asso da ke karamar hukumar Jama’a da ke shiyyar kudancin Kaduna a ranar Talata da daddare.

Wani da ke garin da abin ya faru ya shaidawa Aminiya bayan ya bukaci a sakaye sunansa cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 da minti 10 a daren Laraba (Talata da daddare) daidai gadar Asso inda wasu mahara da ba a tantance ko daga ina suka fito ba su ka farmaki mutanen inda suka kashe mutum guda nan take.

“Wanda aka kashen sunansa Godwin Monday Dogo wanda ya fito daga kauyen Gabi da ke makwabtaka da su sai kuma Shagari Emmanuel, wanda shi kuma aka jikkata inda yanzu haka ya ke karban magani a Asibitin Seth Thomas da ke garin Asso.” Inji shi

Majiyar ta tabbatarwa da Aminiya cewa jami’an tsaron sojoji da suka isa garin suna ci gaba da kula da kai komon jama’a yayinda sauran harkoki ke ci gaba da gudana.

Yayin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo bai amsa wayar ba yayin rubuta wannan rahoton kamar yadda bai amsa sakon kar ta kwana da ya tura masa ta waya ba.